An Gudanar Da Addu’a Ta Musamman Ga ‘Yan Jaridar Da Suka Rasa Rayukan Su A Jos

NUJ

Daga Mohammed Ahmed Baba, Jos

An gudanar da addu’a ta musamman a babban masallacin Juma’a na garin Jos, inda tsohon ministan sadarwa a Nijeriya, Alhaji Ibrahim Dusuki Nakande ya jagoranci ‘yan jarida, wanda babban Limamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam ya jagoranta.

An gudanar da addu’ar ta musamman ne akan ‘yan jaridun da suka rasa rayukan su a bakin aiki da kuma wadanda suke gudanar da aikin a halin yanzu da niyyar Allah ya kare su a bakin aikin su.

Tsohon ministan Alh Ibrahim Dusuki Nakande ya gana da manema labarai, inda ya bayyanna cewa ya kamata ‘yan jarida su gudanar da aikin su yadda ya kamata, da bin dokar aikin da bawa kowani bangare hakkinsa, kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu da talibijin da rediyo akan su yi aikin su yadda ya kamata. Ya ce sau da yawa wasu jaridu da kafafen sadarwa sukan bayar da rahotanni daidai da ra’ayin masu kafafen sadarwar.

Duk rahotannin da za su bayar su tabbatar ingantattu ne inda za a samu zaman lafiya, musamman ganin yadda kasar take cikin rashin tsaro, kafafen jaridu talibijin rediyo daban-daban ne suka halarci addu’ar ta ranar Juma’a.

Exit mobile version