Daga Bello Hamza
A jiya Laraba ne al’umma da dama su ka samu halartar addu’ar cika kwanaki bakwai da rasuwar Malam Umar Abubakar Chiroma Hunkuyi, Editan Labarai na LEADERSHIP A YAU.
An dai gudanar da addu’ar ne a kofar gidansa da ke Layin Abuja a unguwar Rigasa da ke garin Kaduna da kuma Layin Mangwarori da ke Hayin Dogo Samaru a Zariya duka a lokaci daya.
A cikin jawabinsa bayan kammala addu’ar, Malam Ibrahim Musa ya yi kira ga zuriyar da marigayin ya bari da su hada kansu, su kuma tsayu a kan kyawawar tarbiyar da ya dora su a kai.
“Yakamata ku zama tsintsiya madaurinki daya. Ta haka za ku ci ribar zaman duniya ku kuma tsayuwa a kan kyawawar tarbiyar da ya dora ku a kai,” in ji shi.
A garin Samaru kuma tun da sanyin safiya ne dimbin jama’a su ka taru a kofar gidansu da ke Layin Mangwarori a Hayin Dogo, inda a ka gabatar da saukar Alkur’ani Mai Tsarki, inda daga nan ne Liman Umar Sambo da Malam Lukman Alfa su ka jagoranci sauran malamai wajen gabatar da addu’ar neman gafara da rahama ga ruhin Marigayi Malam Umar Chiroma.
Shi dai Malam Umar dan asalin garin Hunkuyi ne da ke karamar hukumar Kudan ta Jihar Kaduna; karatu da aikin gwamnati su ka kawo shi Samaru Zaria, daga baya kuma ya dawo garin Kaduna, inda Allah ya karbi rayuwarsa a ranar Laraba 16 ga Disamba, 2020.
Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya 16. Allah ya gafarta ma sa. Amin.