An Gudanar Da Gasar Matasa Masu Fasaha A Katsina  

Matasa

Daga Sagir Abubakar

Gwamnatin Jihar Katsina ta jadda da kudirinta na zakulo matasa masu hazaka domin karfafa masu fasaha wajen ci gaban jihar.

Jami’in da ke kula da shirin zakulo masu fasaha na jiha, Arch Faisal Jafar Rafin Dadi ya bayar da wannan tabbacin a lokacin bude gasar nuna fasaha ta matasa wanda ya gudana a dakin taro na makarantar kimiyyar sadarwa ta zamani da ke Katsina.

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnati ta bullo da shirin zakulo matasa masu fasaha domin bunkasa kayan da ake samarwa na cikin gida don ci gaban tattalin arziki.

Arch Faisal ya kuma hakikance cewa shirin zai karfafa gwiwar matasa wurin nuna baiwar da Allah ya yi masu domin jawo hankalin masu zuba jari wanda zai habbaka tattalin arzikin jihar.

Jami’in ya lisafto wasu daga cikin nasarorin da shirin ya samu da suka hada da daukar daliban da suka kammala jami’a da mataki mai daraja ta daya aiki a Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa da ke Katsina da kuma tallafin karatu zuwa kasashen waje ga matasa guda biyar da gwamnatin jiha tayi.

Kamar yadda ya ce, gasar ta kunshi rukuni daban-daban da suka hada da fasahar sadarwa ta zamani, zane-zanen kayan gargajiya da wake-wake da dai sauransu.

Da yake jawabi, babban Alkalin gasar, Arch Mansir Kurfi ya zayyano wasu daga cikin muhimman abubuwan da ake bi wajen fitar da wadanda suka yi fice, wanda suka hada da muhimmancin shi da kuma alakarshi da al’adun al’ummar Jihar Katsina.

Arch Mansir Kurfi ya kuma karfafa gwiwar matasa da su shiga cikin gasar domin habbaka harkar kirkire-kirkire a jihar.

Exit mobile version