An Gudanar Da Taron Addu’o’in Neman Zaunar Da Nijeriya Lafiya A Legas

Lafiya

Daga Bala Kukkuru,

Sarkin al’ummar hausawa mazauna yankin karamar hukumar Aja da ke cikin birnin Legas, Alhaji Ibirahim Goma ya gudanar da taron yin adduo’in nema wa Nijeriya karin zaman lafiya da kuma walimar taya shi murnar karuwar aure da ya samu a garin Adamawa bayan kwanakin baya, an kuma gabatar da addu’oin ne a a gidan Filawa Abraham Adesoya ta unguwar Aja a ranar Lahadi da ta gabata.

Taron wand ya kunshi malamai da Sarakunan al’umma daban-daban da sauran al’umma mazauna wadansu unguwarni a cikin birnin Legas, Malam Mohammed Limamin fadar sarkin hausawan Aja shi ne ya jagoranci sauran malamai suka gudanar da adduo’in guda biyu.

Mahalarta taron sun hada da Sarkin Barebarin Jihar Legas, Alhaji Mele Abacha da Alhaji Ummaru Zannan Festak da Sarkin Barebarin unguwar Igwafo da Sarkin Hausawan Mile12, Alhaji da sauran sarakunan al’ummar hausawa da suka fito daga unguwarni  daban daban na cikin birnin Legas, bayan malamai sun kammala adduoin guda biyu ne Sarkin Barebarin Jihar Legas Alhaji Mele Abacha ya Isar da sakonsa da fatan alheri ga Sarkin Hausawan Aja Alhaji Ibirahim Goma da kwamitin da ya shirya wannan taro na gudanar da adduoin guda biyu karshe yayi kira ga masu hannu dashuni dasu rika shirya taro na gudanar da irin wadannan adduoin na nemar ma Nijeriya Karin zaman lafiya.

Sarkin al’ummar hausawan mazauna unguwar ta Aja Alhaji Ibirahim Goma ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka samu halartar taron.

Exit mobile version