Bello Hamza" />

An Gudanar Da Zabe A Karamar Hukumar Kudan Cikin Lumana

An bayyana cewa, ganin yadda al’ummar karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna suka fito kwansu da kwarkwatar su don kada kuri’arsu ba tare da wani tashin hankali ba, ya nuna cewa, yanayin gudanar da siyasa a karamar huukumar ya kara samun tsafta in aka kwatanta da shekarun baya, wannna furuci ya fito ne daga bakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Shu’aibu Bawa Jaja a tattaunawarsa da wakilinmu jim kadan bayan ya kammala zagayen wasu runfunar zabe a garin Kudna da kewaye, ranar Asabar da ta gabata yayin gudanar da zaben shugaban kasa dana majalisun kasa da aka gudanar a fadin Nijeriya 23 ga watan Fabrairu 2019.
Alhaji Shu’aibu Bawa Jaja ya nana cewa, an samu wannna nasarar ce sakamakon fadarkarwa da shugabannin al’umma, musammnan sarakunan gargajiya da malaman addini suka dukufa wajen yi wa al’umma, a koda yaushe, ya kuma yaba da yadda suka tsara kansu da kuma yadda suke jefa kuri’arsu ba tare da tashin hankali ba.
Daga nan kuma ya yi kira ga a’lumma musamman matasa da su rungumi zaman lafiya muasamman a lokacin da aka sanar da sakamakon zabe, shirin da hukmar zabe ta yi na sanar da sakamako zabe tun daga matakin akwati har zuwa mazaba zai yi matukar taimakawa, don dukkan magoya bayan dan takara za su kwana da sanin abin da dan takararsu ya samu, hakan zai sa kowa ya san abinda ya samu, in kuma ya fadi zabe ba zai zamana ya tayar da hankalinsa ba, don kuwa abin da yake haifar da tashin hankali a wasu lokutta shi ne tunanin an murde musu nasarar da suka samu” inji shi.
Daga karshe ya yaba wa hukumar zabe ta INEC da jami’an tsaro a bisa yadda suka gudanar da harkokin zaben, a kan haka ya bukaci su tabbatar da sun gudanar da sauran zabukkan dake tafe ba tare da nuna banbanci ba, “Hakan zai kara wa mutane kwarin gwiwa da kuma fata a kan hukumomin kasar nan baki daya” inji shi.

Exit mobile version