Jamil Gulma" />

An Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali A Kebbi

Jihar Kebbi ita ma ta bi sawun jihohin Nijeriya wajen zaben Shugaban kasa da yanmjalisar tarayya da kuma majalisar wakilai da hukumar zabe mai zaman kanta ta date daga 16 ga wannan watan na Fabrairu watan zuwa Assabar 16 ga wannan watan na Fabrairu 2016.
Wakilinmu ya zagaya wadansu mazabu don ganewa idonsa inda ya zanta da mutane kamar haka.
Santa Dokta Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta arewa kuma har wa yau dantakarar Sanata a karo na biyu jim kadan bayan ya jefa kuri’arsa ya bayyana gamsuwarsa bisa ga yadda mutane kwansu da kwarkwata suka fito don jifar kuri’a kuma a tsanake babu tashin hankali wanda ya ke ya nuna aikin gwamnati na wayarda kan mutane ya yi tasiri saboda babu wani ci zarafin juna.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka sami nasarar lashe zaben da su hada kai su yi aiki tare don kara kawo cigaban al’umma ta fannoni dabam-dabam.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sa a kammala zabe lafiya.
Shi kuma Alhaji Suleiman Muhammad Argungu Shugaban maiakata a gidan gwamnatin jihar Kebbi ya bayyana irin jin dadinsa bisa ga yadda mutane suka fito wanda a cewarsa a tarihin zabe bai taba ganin mutane sun fito jifar kuri’a kamar wannan lokacin ba wanda a sanadiyyar yawan mutane rumfar da ya ke jifar kuri’a da ke anguwar law cost an kasa ta zuwa kashi biyar wanda kuma kowane kashi yana da sama da mutane 500.
Ya yi kira ga jami’an zabe da su yi hakuri da jama’a saboda akwai tsofaffi da kuma wadanda ke da rauni da kuma wani lokaci ita kanta na’urar tantancewa tana dan daukar lokaci wajen tantance wadansu mutane.
Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi wanda kuma jigo ne a jam’iyyar PDP ya ji dadin irin yadda aka fito don jefa kuri’a, ya kuma ja hankalin ma’aikatan zabe da su ji tsoron Allaha wajen aiwatar da ayukan su saboda amana ce aka danka a hannunsu, sannan kuma duk wanda Allah ya baiwa nasarar lashe zaben da ya yi wa al’umma adalci wajen shugabanci ko kuma wakilci.
A nasa bayanin shi kuma Sanata Isah Galaudu kuma dantakarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP ya ce ya gamsu da irin tsarin da jami’an tsaro suka shirya da yadda zaben ke gudana saboda hukumar zabe ta kai kaya kuma an soma ayukka yadda ya kamata, ba shakka mutane sun amsa kira kuma sun fito su zabi mutanen da suke ganin za su fitar da su daga kangin da suka sami kansu ciki na tawaya, wannan wahala da mutane suka.sami kansu a ciki tana cikin dalilan da suka sanya suka yi cincirindo a rumfunan zabe don su kawar da wannan gwamnati da a sanadiyyar wannan shugabanci na ta talauci ya yi wa jama’a katutu a sanadiyyar rashin aikin yi da kuma kariyar jari.

Exit mobile version