Connect with us

LABARAI

An Gudunar Da Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina

Published

on

Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta gudanar da Zaben shuwagabanninta a matakin jihar wanda fiye da masu kada kuri’a dubu sha daya suka amince da tsofafin shuwagabanni da su koma akan mukaminsu karo na biyu.

Yanzu haka dai mutun talatin da shida ne aka amicewa komawa akan karagar mulki inda mukadashin shugaban jam’iyyar APC A jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu ya zama shugaba mai cikakken iko na jam’iyyar APcC a jihar Katsina a ya yin da Ahmadu Dan-Malam ya samu mukamin mataimakin shugaba.

Sauran da aka amince da su a matsayin shuwagabanni sun hada da mataimakin shugaba mai kula da shiyyar  Daura Ahmad Sani sai kuma mataimaki mai kula da shiyyar Futuwa Bala Abubakar Musawa sai mataimaki mai kula da shiyyar Katsina ta tsakiya Ado Usman tare da Ahmad Sani a matsayin sakatara na jam’iyyar da sauran muakamai daban-daban

Zaben dai ya gudana bisa kulawa tare da sa idon shugaban hukumar zabe ta kasa reshen jihar Katsina  Alhaji Jibril Zarewa tare da shugawabannin jam’iyyar a matakin kasa da kuma dubun dubatar jama’a a filinnwasa na Muahammadu Dikko da ke Katsina

Da yake nasa jawabin shugaban kwamitin zabe wanda uwar jam’iyya ta turo daga Abuja Malam Usman Muhammad ya bayyana wannan daidaito da aka samu a ya yin gudanar da Zaben a matsayin nuna adalci da kuma baiwa kowa hakkinsa wanda daman jam’iyyar ta yarda da sasanci a matsayin zabe.

Ya kuma yabawa mambobin jam’iyyar tare da shugabancinta a matakin jihar Katsina musamman yadda aka nuna da’a da biyyaya a ya yin gudanar da wannan zabe.

Shima  a nasa jawabin sabon shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu ya yi alkawarin tafiya da kowane dan jam’iyya tare da bada tabbaci ga shugabancin jam’iyyar na kasa cewa zai jagoranci jam’iyyar APC wajan samun nasarar zabe mai zuwa a shekarar 2019 idan Allah Ya Kaimu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: