An Gurfanar Da Daliba Kan Damfarar Abokan Karatunta

Makanike

An gurfanar da wata dalibar jami’ar Adekunle Ajasin, a gaban wata kotun majistire da jihar Ondo, saboda zargin da ake yi mata na damfarar wasu kudi.

Dalibar wadda ke shekarar karatu ta uku, a jami’ar, sashen koyon aikin jarida, ta gurfana a gaban kotu bisa zargin damfarar wasu mutum biyar tsabar kudi naira N486,000

Dalibar mai kimanin shekara 26, wadda ke zama a shagon ‘kafe’ an zarge ta da aikata wannan laifi a Alagbaka.

Kamar yadda mai gabatar da kara, Insifeto Akintimehin Nelson ya ce, Fadare ta yi zambar N486,000 da sunan za ta taimaka wa masu su biya kudin makarantar ‘ya’yansu.

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, mai gabatar da karar ya bayyanawa kotu cewa, Fadare ta karbi N75,500 daga hannun Omoteji Israel ta asusun ajiyarsa na banki, mai lamba 0175044918 da ke ‘Guaranty Trust Bank’.

Haka kuma, mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa, wadda ake zargin ta kuma karbi N150,000 daga wajen Eunice Bamidele da sunan za a ba ta kudi don ta biya wa ‘yarta kudin makaranta, haka kuma ta sake karbar N155, 000 daga wajen Gbenga Adebayo da kuma wasu N55,000 daga Esther Oluwatoki da niyyar za ta taimake su, su biya kudin makarantar yaransu cikin sauki.

Akintimehin ya kara da cewa, Fadare ta yi zanbar N51,000 domin ta yi amfani da su daga hannun Oyinbodunmi Ibikunle donin ta taimaki shi wajen biyan kudin makaranta.

Saboda haka, wannan laifi ne da ya sabawa sashi na 418, 419, 383, 390 (9), 465, 467 da kuma 338 na dokar aikata laifuka,ta shekarar 2006.

Lauyan wadda ake karar, Barista Bernard Godwin, ya roki kotun da ta bayar da belin Fadare saboda ba a tabbatar da laifukan da ake zarginta da su ba.

Saboda haka, alkalin kotun Musa Al-Yunnus, ya amince da bayar da belin  a kan kudi N500,000, da kuma wadanda za su tsaya mata mutum biyu. Haka kuma ya ce, wadanda za a ba su belin, sai sun kawo takardar haraji ta shekara uku. Yanzu haka an dahe sauraron karar zuwa ranar 28, Janairu 2022.

Exit mobile version