An gurfanar da wani dalibi mai suna Patrick Moses dan shekaru 23 a kotun dake zama a Kuje Abuja, bisa zargin satar waya kirar Tecno, wanda kudin ta ya kai Naira 80,000, Moses wanda yake Anguwar Grade da zama, zai fuskanci tuhumar laifukka biyu, wato laifin sata dana shiga gida ba bisa ka’ida ba.
Dan sanda mai shigar da kara, Doris Okoroba ya shaida wa kotu, yadda Mista Alfa Sule ya kawo musu karar Patrick a ofishin su dake Kuje a ranar 10 ga watan Oktoba, ya bayyana yadda Moses ya shiga gidan Sule ba bisa ka’ida ba, inda ya sace mishi waya, amma anyi nasarar cafke shi a lokacin da yake kokarin siyarda wayar ga wani mai gyaran waya.
Mai shigar da kara yace laifukkan sun saba da sashe na 287 da 326 na dokar shara’a, amma wanda ake zargin ya musanta duk tuhumar da ake mishi, a karshe alkali ya bada belin wanda ake zargin a kan kudi Naira 50,000, da kuma wanda zai tsaya a maimakon wanda ake zargin, daga bisani an daga karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba.