Umar A Hunkuyi" />

An Gurfanar Da Jami’ar Tallace-Tallace A Bisa Zarginta Da Satar Kudin Kamfani

A jiya Litinin ne aka gurfanar da wata jami’ar tallace-tallace mai suna, Maris Adjebrefe, mai shekaru 31, a gaban Kotun Majistare da ke Ikeja, a bisa zarginta da satar kudaden talla har Naira 900,000 daga kamfanin da take yi wa aiki. Wacce ake tuhumar da take zaune a Anguwar Igando, ta birnin Legas, ana tuhumarta ne da aikata sata da kuma cin amana, laifin da ta musanta aikatawa.
Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Raji Akeem, ya shaidawa kotun cewa, ta aikata laifin ne a ranar 5 ga watan Maris, a kamfanin, Prothribe Astute Height Ltd. Kamfanin da ke zaune a gida mai lamba 57, Sumonu St., Oke-Ira, Ogba, Lagos. ”Adjebrefe tana aiki ne tare da kamfanin na, Prothribe Astute Height Ltd. An kuma baiwa kamfanin wasu kaya ne domin ya siyar ga abokanin huldar sa.”
“Sai kuma, ita sai ta zame Naira 900,000, daga kudaden cinikin kayan da aka sayar ba tare da ta zuba su a cikin asusun kamfanin ba, amma sai ta mayar da su zuwa amfanin kanta,” in ji mai gabatar da karan.
Alkalin kotun, O. A. Layinka, ta bayar da belin wacce ake karan a kan tsabar kudi Naira 200,000, tare da mutane biyu masu tsaya mata su ma a kan wannan kudin. Daganan sai ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Mayu.

Exit mobile version