Umar A Hunkuyi" />

An Gurfanar Da Maigadi Bisa Satar Kwamfutar Bako A Otal

A ranar Talata ce, aka gurfanar da wani mai gadi a gaban kotu mai daraja ta 1 da ke Kabusa, Abuja, a bisa zargin da ake yi masa na satar Kwamfutar Laptop, kirar HP, wacce aka kiyasta kudin ta a kan naira 200,000, ta wani bako da ya sauka a Otal din da yake gadi a cikin sa.

‘Yan sanda suna tuhumar Philip Oche,23, da Harisu Aliyu,26, ne da hada baki da kuma yin sata.

Mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa, Mista Ejikeme Omeji, ne ya kawo rahoton maganar a ofishin ‘yan sanda da ke Asokoro, Abuja, a ranar 26 ga watan Afrilu.

Lawal ya yi zargin cewa, an fasa motar wanda ya kawo karan ne kirar Toyota land Criser, wacce ya ajiye a gaban Otal din na Jeniferia Hotel, Asokoro, Abuja.

Ya ce, sai aka sace Kwamfutar kirar HP, wacce kudin ta ya kai naira 200,000 da kuma jikar kwamfutar da kudn ta ya kai naira 90,000.

Sai dai dukkanin wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin da ake tuhumar na su da aikatawa.

Alkalin kotun, Ibrahim Kagarko, ya bayar da belin mutanan da ake tuhumar a kan kudi naira 500,000 tare da mutum guda da zai tsaya masu shi ma a kan wannan kudin.

Kagarko, ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Agusta.

Exit mobile version