An gurfanar da wani makanike mai suna Idris Bashir mai shekara 28 a duniya a gaban kotun yanki mai daraja ta daya dake karu a yankin Abuja bisa lafin satar wayar hannu.
Wanda ake zargin mazaunin unguwar Lugbe, Abuja, yana fuskantar tuhumar shiga wuri ba tare da izini ba da kuma sata, ya dai musanta aikata laifin a yayin da aka karanto masa laifin.
Mai gabatar da karar, Ayotunde Adeyanju, ya bayyana wa kotun cewa, wata ne mai suna Joy Ugbor da ke FHA Karu, Abuja, ta kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda da ke Karu ranar 17 ga watan Nuwamba.
“Ta bayyana cewa, a wannan ranar ne tana zaune a cikin shagon ta rike da wayar ta kirar Gionee F250 da aka kiyasata kudinsa ya kai N60,000, inda wanda ake zargin ya shigo ya dauki wayar ya hau mashin dinsa ya gudu da ita, bayan an bi shi ne aka samu nasarar kama shi,” inji Adeyanju.
Ya kuma bayyana cewa, laifin ya saba wa sashi na 348 da 288 na dokar fanal cot.
Alkalin kotun, Inuwa Maiwada, ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi N100, 000 ya kuma daga karar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu don ci gaba da sauraron shari’a.
Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar...