An Gurfanar Da Mataimakin Kwamandan Hisba A Kotu

Hisbah

Hispah Sharia Police, a volunteer religious militia force, enforcing Sharia law. The implementation of Islamic Sharia Law across the twelve northern states of Nigeria, centres upon Kano, the largest Muslim Husa city, under the feudal, political and economic rule of the Emir of Kano. Islamic Sharia Law is enforced by official state apparatus including military and police, Islamic schools and education, plus various volunteer Militia groups supported financially and politically by the Emir and other business and political bodies. Fanatical Islamic Sharia religious traditions are enforced by the Hispah Sharia police. Deliquancy is controlled by the Vigilantes volunteer Militia. Activities such as Animist Pagan Voodoo ceremonies, playing music, drinking and gambling, normally outlawed under Sharia law exist as many parts of the rural and urban areas are controlled by local Mafia, ghetto gangs and rural hunters. The fight for control is never ending between the Emir, government forces, the Mafia and independent militias and gangs. This is fueled by rising petrol costs, and that 70% of the population live below the poverty line. Kano, Kano State, Northern Nigeria, Africa

Daga Mustapha Ibrahim Kano

Wani magidanci da ke zaune a karamar hukumar Danbatta, ya kai karar Malam Auwalu Sabo, wanda kuma shi ne mataimakin kwamandan Hisba na karamar hukumar Dambatta da ke jihar Kano, kan kotu ta bi masa hakinsa kan shiga gidansa ba tare da izininnsa ba, shi dai Auwalu Sabo ya yi kamar dai yadda kotu karkashin mai shari’a Malam Abdu Abdullahi wayya, Alkalin babban  kotun shari’ar Musulinci da ke Hotoro ta fara sauraran karar kan wannan zargi na magidanci mai suna Sunusi Usman Dan Koro, a ranar Litinin da ta gabata.

Sai dai kuma lauyan wanda ake zargi da  shigar gidan Sunusi Usman dan koro ya musanta wannan zargin da ake yi wa mataimakin kwamandan Hisba na Danbatta, inda kuma ya nemi kotu ta bayar  da belin wanda ake zargi kuma ta ta ba da bilin Auwalu Sabo kamar dai yadda lauyansu ya nema.

Sai dai kuma a wani labarin daga hukumar Hisba ta Kano na cewa, yanzu haka hukumar na da motar Tirila biyar na giya  a ajiye a hukumar wanda hisba ke sauraran izini daga kotu don bankawa giyar wuta kamar yadda  dokar haramta sha, da siyar da barasa take  a Kano.

A cewar babban kwamanda Hisba na Kano Sheikh Haruna Ibn Sina ya fada a wani taro da hukumar ta yi a Kano. Inda shi kuwa mai ba wa gwamna Kano shawara kan harkar addini Hon. Ali Baba Agama Lafiya ya ce mata yan Hisba sun fi maza ‘yan hisba jarumtar aikin Hisba.

Exit mobile version