Connect with us

MANYAN LABARAI

An Gurfanar Da Mutum Biyu Bisa Zargin Satar Tayoyin Mota A Kotu

Published

on

An gabatar da wasu mutum biyu a kotun majestiri dake jihar Ogun, bayan an zarge su da satar tayoyin mota har guda 46 wanda kimar kudinsu ta wuce Naira miliyan uku.

Wadanda ake zargin su ne Muhammad Umar mai shekaru 30 da Jidda Adam dan shekaru 40, ana tuhumar su da laifin sata, da zagon kasa, basu kadai ake zargi ba, amma zuwa yanzu dai su kadai ne a hannun hukumomi.

Wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 17 ga watan Agusta da misalin karfe day zuwa hudu na dare, sun yi kokarin balle kofar inda aka ajiye tayoyin motar ne, inda masu gadin wajen suka samu nasarar cafke su, sauran kuwa suka arce. Zuwa yanzu kotu ta bada belinsu inda aka daga sauraren karar zuwa ranar 27 ga wannan watan na Satumba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: