An Gwada Lafiyar Jadon Sancho A Manchester United

Jadon Sancho

Dan wasa Jadon Sancho yana daf da kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United kan fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund, bayan da aka auna koshin lafiyarsa ranar Talata.

Ranar 1 ga watan Yuli manchester  United ta amince da kudin da Dortmund ta gindaya kan dan wasan mai shekara 21 a duniya, amma sai da aka kammala gasar Euro 2020, sannan za a karkare cinikin.

Ranar Talata Sancho ya je filin atisayen Manchester United da ke Carrington da sanyi safiya, ana kuma sa ran kungiyar za ta sanar da karkare komai cikin makon nan sannan ya fara hutu bayan ya fafata a gasar turai.

Sancho tsohon dan kwallon Manchester City yana daga cikin wadanda suka kasa ci wa Ingila fenareti a gasar Euro 2020 da ta kai Italiya ta lashe kofin kuma sauran da suka barar sun hada da Bukayo Saka da kuma Marcus Rashford, bayan da suka tashi 1-1 a Wembley ranar Lahadi.

Dan kwallon abokine ga dan wasa Phil Foden na Manchester City tun kafin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Dortmund a shekarar 2017, sai dai Sancho bai buga wa babbar kungiyar ta City wasanni ba.

Babban wasa da ya buga a Ingila a kungiya shine wanda kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta doke kungiyarsa Dortmund a filin wasa na Wembley a cikin watan Fabrairun shekara ta 2019.

Sancho ya yi rauni a karawa biyu tsakanin Dortmund da Manchester City a kuarter-final a Champions League a kakar da ta kare wanda hakan yasa bai fuskanci tsohuwar kungiyar tasa ba.

Exit mobile version