Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

An Halaka Soja Daya Da Mutum Biyu Yayin Artabun Kwastom Da Masu Fasa Kwauri

by Khalid Idris Doya
November 23, 2020
in LABARAI
2 min read
Masu Fasa Kwauri
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mutum uku ciki har da Soja mai mukamin Lieutenant, Josiah Peter ne aka bada rahoton kashesu yayin wani artabu a tsakanin Kwauri Hukumar Hana Fasa Kwauri wato (Kwastam) da wasu ‘yan fasa Kwauri masu shigo da kaya ba bisa ka’ida ba a Igbo-Ora da ke jihar Oyo ranar Juma’a.

Majiyarmu ta habarto cewa an samu aukuwar arangamar ne a tsakanin jami’an Kwastam masu aiki Shiyyar Zone A, da masu fasa Gwabri a Ogbo-Ora da ke jihar Oyo.

samndaads

Kakakin ‘yan sanda jihar Olugbemiga Fadeyi shine ya tabbatar da faruwar lamarin na mutuwar sojan da wasu mutum biyu a rigimar.

Fadeyi ya ce ‘yan sanda sun kaddamar da bincike domin gano hakikanin dalilin da ya janyo fadar a tsakanin Kwastam da wasu da ake zargin masu fasa Kwauri ne a Igbo-Ora wanda ya janyo mutuwar Lieutenant din soja guda sakamakon harbin da aka masa.

Shi ma da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, jami’ai hulda da jama’a na Kwastam reshen shalkwatansu ta shiyya da ke Oyo/Osun, Kayode Wey ya shaida cewar ya na sane da abun da ya faru amma ba zai iya bada cikakken bayanin da ya faru ba kawo yanzu.

Da a ka tambaye shi kan batun kisa, ya ce, ba zai iya tabbatar da mutuwar kowa a harin ba.

“Eh, ina da masaniya. Na ji labarin abun da ya faru ne a bakin wani. Don haka ni ba zan iya bada cikakken bahasin lamarin ba a daidai wannan lokacin,” in ji shi.

Wani mazaunin Igboora ya nakalto cewa sun ji karar harbe-harbe a sama a lokacin fadar, wanda a sanadiyyar hakan wani makwabcinsi daya, soja daya da jami’in kwastam suka rasa rayukansu sakamakon harbin bindiga da suka gamu da su.

Ya ce, mutum uku din sun mace a sakamakon wannan Harbin, yayin da wasu kuma suka gamu da raunuka daban-daban sakamakon wannan arangamar ta Kwastam da masu fasa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kungiyoyi Sun Fi Dan Majalisa Kawo Cigaba A Karamar Hukumar Mani – Hon. Abubakar Jani

Next Post

Sai Da Kyawawar Tarbiya Matasa Za Su Zama Nagari – Ustaz Na’ibi Lokoja

RelatedPosts

Sace Daliban Kagara: Gwamnatin Tarayya Ta Bar Mu Da Jidali Mu Kadai – Gwamna Sani

Sace Daliban Kagara: Gwamnatin Tarayya Ta Bar Mu Da Jidali Mu Kadai – Gwamna Sani

by Khalid Idris Doya
4 mins ago
0

Daga Khalid Idris Doya A cigaba da kokarin gwamnatin jihar...

Jana’izar Sojojin Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgi Ta Gudana Cikin Alhini

Jana’izar Sojojin Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgi Ta Gudana Cikin Alhini

by Khalid Idris Doya
4 mins ago
0

Daga Khalid Idris Doya An yi jana’izar dakarun rundunar sojojin...

Majalisar Bayelsa Ta Yi Kudirin Dokar Dabaibaye Kiwo Da Sana’ar Dabbobi  

Majalisar Bayelsa Ta Yi Kudirin Dokar Dabaibaye Kiwo Da Sana’ar Dabbobi  

by Khalid Idris Doya
11 mins ago
0

Daga Abubakar Abba Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ta gabatar da...

Next Post
Ustaz Na'ibi Lokoja

Sai Da Kyawawar Tarbiya Matasa Za Su Zama Nagari – Ustaz Na'ibi Lokoja

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version