Khalid Idris Doya" />

An Halaka Soja Daya Da Mutum Biyu Yayin Artabun Kwastom Da Masu Fasa Kwauri

Masu Fasa Kwauri

Mutum uku ciki har da Soja mai mukamin Lieutenant, Josiah Peter ne aka bada rahoton kashesu yayin wani artabu a tsakanin Kwauri Hukumar Hana Fasa Kwauri wato (Kwastam) da wasu ‘yan fasa Kwauri masu shigo da kaya ba bisa ka’ida ba a Igbo-Ora da ke jihar Oyo ranar Juma’a.

Majiyarmu ta habarto cewa an samu aukuwar arangamar ne a tsakanin jami’an Kwastam masu aiki Shiyyar Zone A, da masu fasa Gwabri a Ogbo-Ora da ke jihar Oyo.

Kakakin ‘yan sanda jihar Olugbemiga Fadeyi shine ya tabbatar da faruwar lamarin na mutuwar sojan da wasu mutum biyu a rigimar.

Fadeyi ya ce ‘yan sanda sun kaddamar da bincike domin gano hakikanin dalilin da ya janyo fadar a tsakanin Kwastam da wasu da ake zargin masu fasa Kwauri ne a Igbo-Ora wanda ya janyo mutuwar Lieutenant din soja guda sakamakon harbin da aka masa.

“Bayanai sun nuna cewa masu fasa Kwauri ne suka farmaki jami’an Kwastam a Igbo-Ora. A kokarin kai dauki ga jami’an kwastam da aka kai wa harin, wani soja mai mukamin Lieutenant Josiah Peter ya gamu da harbin bindiga daga bisani ya mutu. Sai dai an kaddamar da fara bincike kan lamarin,” ya shaida.

Shi ma da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, jami’ai hulda da jama’a na Kwastam reshen shalkwatansu ta shiyya da ke Oyo/Osun, Kayode Wey ya shaida cewar ya na sane da abun da ya faru amma ba zai iya bada cikakken bayanin da ya faru ba kawo yanzu.

Da a ka tambaye shi kan batun kisa, ya ce, ba zai iya tabbatar da mutuwar kowa a harin ba.

“Eh, ina da masaniya. Na ji labarin abun da ya faru ne a bakin wani. Don haka ni ba zan iya bada cikakken bahasin lamarin ba a daidai wannan lokacin,” in ji shi.

Wani mazaunin Igboora ya nakalto cewa sun ji karar harbe-harbe a sama a lokacin fadar, wanda a sanadiyyar hakan wani makwabcinsi daya, soja daya da jami’in kwastam suka rasa rayukansu sakamakon harbin bindiga da suka gamu da su.

Ya ce, mutum uku din sun mace a sakamakon wannan Harbin, yayin da wasu kuma suka gamu da raunuka daban-daban sakamakon wannan arangamar ta Kwastam da masu fasa.

Exit mobile version