Connect with us

KASASHEN WAJE

An Hana Mutane Cin Kare Da Kule a Garin Hanoi Na Vietnam  

Published

on

A Vietnam an hana mutanen da ke zama a garin Hanoi cin kare da kule dan hanyar da suke bi wajen yanka su na bata sunan garin kuma zai iya kawo cuta ga jama’ar garin.

Mutanen garin na son naman kare da na kule wai a ganin su yana sasu karfin jiki.

Shugaban garin mai suna Nguyen Van Suu ya ce hanyar da mutanen garin ke bi wajen yanka dabbobin zai jawo wa garin bakin ciki musamman a idon baki yan yawon shakatawa

Nguyen ya umarci hukumomin garin Hanoi da su sanar da jama’ar garin hadarin da ke tattare da cin naman karnuka da kule.

Akwai karnuka da maguna a garin da yawan su ya kai 493,000, ana kiwon da yawansu a gida a matsayin dabbobin gida, a yayin da wani adadin na dabbobin ake kiwo da su don a ci namansu.

Jama’ar Vietnam na matukar son cin naman kare da na mage, duk da jama’a na kara samun wayewar kai wajen daina cin naman dabbobin sai dai su ajiye su a matsayin dabbobin kiwo.

‘Hanyar da ake bi wajen yanka dabbobin yana iya zubar wa da jama’ar birnin mutumci sosai musamman a idon wayayyun mutane a duniya da kuma ‘yan yawon shakatawa da suke ziyartar birnin.’ Inji Nguyen

Ana ganin kusan mutum uku ne suka mutu daga cutar karnukan a garin na hanoi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: