Mahdi M Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home JAKAR MAGORI

An Hana Wani Musulmi Takardar Zama Dan Kasar Jamus Saboda Kin Musabiha Da Mace

by Mahdi M Muhammad
January 6, 2021
in JAKAR MAGORI
2 min read
Musulmi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wata kotu a kasar Jamani ta yanke hukuncin cewa ba za a bai wa wani likita Musulmi takardar zama cikakken dan kasa ba, bayan ya ki musafaha da matar da ta gabatar masa da takardar shedar zama dan kasa.

Likitan dan kasar Labanon din mai shekaru 40 da ba a bayyana sunansa ba wanda ya shigo kasar Jamani a shekarar 2002 ya ki ya girgiza hannun mata saboda dalilai na addini.

samndaads

Kotun da ke garin Baden-Württemberg ta yanke hukuncin cewa wadanda suka ki yarda su yi musafaha saboda fahimtar tsattsauran ra’ayi game da al’adu da addinai, saboda suna yiwa mata wani kallo daban, kuma sun ki amincewa da yin rayuwa daidai da na mutanen Jamani.

Mutumin yana gab da zama Bajamushe bayan ya zauna a kasar tsawon shekaru 13, ya kammala karatun likitanci ya kuma ci jarabawar zama dan kasa tare da babbar alama.

Gwarawar nasa game da hukuncin bai yi nasara ba a gaban Kotun gudanarwar Stuttgart, kuma ya daukaka kara zuwa kotun BGH. Bayan yanke hukuncin a ranar Asabar, kotun ta ce, mutumin zai iya daukaka kara zuwa Kotun gudanarwa ta tarayya saboda muhimmancin shari’ar.

Kotun BGH din ta bayyana musafaha a matsayin gaisuwa ne kawai, wacce ba ta da nasaba da jinsin wadanda abin ya shafa, kuma ana yin hakan sama da karnoni da dama.

Alkalin ya gano cewa, musafahar kuma tana da ma’ana ta shari’a, a cikin wannan alama ce ya kammala yarjejeniya. Amincewa da gaisawa na hannu, yana da tushe sosai a zamantakewar jama’a, al’adu da kuma shari’a, wanda ke tsara yadda muke rayuwa tare, in ji alkalin.

Kotun ta bayyana cewa, duk wanda ya ki musafaha kan dalilan da suka shafi jinsi to ya sabawa daidaito da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Jamani.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

An Cafke Uwa Da Laifin Kulle Danta Tsawon Shekaru 28

Next Post

Akwai Alfanu A Ganyen Rogo, Cewar Wani Kwararre

RelatedPosts

Na'urar ATM

Yadda Ya Makale A Dakin Na’urar ‘ATM’

by Mahdi M Muhammad
18 hours ago
0

A ranar Laraba da yamma ne wani dan kwangila a...

Masarauta

An Yanke Mata Shekara 43 A Gidan Yari Saboda Bata Sunan Masarauta

by Mahdi M Muhammad
18 hours ago
0

An yanke wa wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati hukuncin daurin shekara...

Mabaraciya

Hoto Daya Ya Sanya Mabaraciya Zamo Wa Mashahuriya

by Mahdi M Muhammad
19 hours ago
0

Shekaru hudu da suka gabata, Rita Gabiola wata yarinya ce...

Next Post
Ganyen Rogo

Akwai Alfanu A Ganyen Rogo, Cewar Wani Kwararre

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version