Mahdi M Muhammad" />

An Hana Wani Musulmi Takardar Zama Dan Kasar Jamus Saboda Kin Musabiha Da Mace

Musulmi

Wata kotu a kasar Jamani ta yanke hukuncin cewa ba za a bai wa wani likita Musulmi takardar zama cikakken dan kasa ba, bayan ya ki musafaha da matar da ta gabatar masa da takardar shedar zama dan kasa.

Likitan dan kasar Labanon din mai shekaru 40 da ba a bayyana sunansa ba wanda ya shigo kasar Jamani a shekarar 2002 ya ki ya girgiza hannun mata saboda dalilai na addini.

Kotun da ke garin Baden-Württemberg ta yanke hukuncin cewa wadanda suka ki yarda su yi musafaha saboda fahimtar tsattsauran ra’ayi game da al’adu da addinai, saboda suna yiwa mata wani kallo daban, kuma sun ki amincewa da yin rayuwa daidai da na mutanen Jamani.

Mutumin yana gab da zama Bajamushe bayan ya zauna a kasar tsawon shekaru 13, ya kammala karatun likitanci ya kuma ci jarabawar zama dan kasa tare da babbar alama.

Amma a hawan karshe, ya ki ya gaisawa da matar jami’ar a bikin a shekarar 2015, wanda hakan ya sa hukumomin jihar suka rike masa takardar shedarsa kuma suka ki amincewa su ba shi. Ya yi bayyana cewa ya riga ya yi wa matarsa alkawarin cewa ba zai taba gaisawa da wata mace ba.

Gwarawar nasa game da hukuncin bai yi nasara ba a gaban Kotun gudanarwar Stuttgart, kuma ya daukaka kara zuwa kotun BGH. Bayan yanke hukuncin a ranar Asabar, kotun ta ce, mutumin zai iya daukaka kara zuwa Kotun gudanarwa ta tarayya saboda muhimmancin shari’ar.

Kotun BGH din ta bayyana musafaha a matsayin gaisuwa ne kawai, wacce ba ta da nasaba da jinsin wadanda abin ya shafa, kuma ana yin hakan sama da karnoni da dama.

Alkalin ya gano cewa, musafahar kuma tana da ma’ana ta shari’a, a cikin wannan alama ce ya kammala yarjejeniya. Amincewa da gaisawa na hannu, yana da tushe sosai a zamantakewar jama’a, al’adu da kuma shari’a, wanda ke tsara yadda muke rayuwa tare, in ji alkalin.

Kotun ta bayyana cewa, duk wanda ya ki musafaha kan dalilan da suka shafi jinsi to ya sabawa daidaito da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Jamani.

 

Exit mobile version