An Harbe Wata Mata A kan Hanyarta Ta Zuwa Coci A Ebonyi

A ranar Lahadi ce a ka harbe wata mata har lahira mai suna Chinyere mai shekaru 55, a kan hanyarta ta zuwa Coci, kamar dai yadda majiyarmu ta bayyana mana. Wakilinmu ya labarta mana cewa, a cikin wadanda a ka harbe akwai matar mai ‘ya’ya bakwai da kuma wasu sauran mata biyu, wadanda su ma su na kan hanyarsu ce ta zuwa cocin Solution Ground International Ministries, wadda take a kan hanyar Okigwe Amasiri cikin karamar hukumar Afikpo ta arewa ta Jihar Ebonyi, da misalin karfe biyar na daren ranar Lahadi. Lokacin da su ka isa kofar shiga cocin, matan sun ga wani mutum wadanda su ka gane cewar shi Paul, ne wanda kuma shi ne ya harbe su.

Shugaban da ke lura da ita cocin, Fastor Michael Uche, ya bayyana wa wakilinmu cewar, an sanar da shi ne abinda ya faru. Uche ya bayyana cewar, shi wanda a ke zargin da kai wannan harin ya na son ya harbe mahaifiyar shi ce, ba wai marigayiya Agu ba.  Ya kara jaddada cewar shi wanda a ke zargin dama ya dade da yi wa mahaifiyar shi barazanar cewar zai ci mutuncin ta, saboda da akwai wata matsala da ke tsakanin wanda a ke zargin da kuma ita mahaifiyar tashi.

Da ya ke bayani dangane da shi al’amarin mataimakin Faaston cocin Emmanuel Onyiagha, ya bayyana cewar, su wadanda su ke cocin sun koma taimakon kansu ne, lokacin da su ka gagara samun wani taimako daga runduna ta musamman wadda take yakar al’amarin fashi da makami, saboda a samu ceton ita matar. Onyiagha ya bayyana cewar, Agwu an kai ta asibitin Mater da ke Afikpo, inda a ka gane cewar an harbe ta wurare da yawa, sakamakon haka sai ta mutu.

Da ta ke tabbatar da aukuwar al’amarin, jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Lobeth Odah, ta bayyana cewar, shi wanda a ke zargin wanda a ke kira da sunan Paul Okoudu, an kama shi tuni. Kamar dai yadda ita jami’ar hulda da jama’a ta bayyana, za a gurfanar da wanda a ke zargi a kotu idan an kammala binciken kuma a ka tabbatar da cewar ya aikata laifin. Ta kara bayyana cewar, “Rahoton da ke gabanta ya bayyana cewar, ya yi amfanine da bindigar gida wajen harbe matar.

“Mu na kira da mazauna Ebonyi su taimaka da bayanan da za su taimaka a kan duk wanda a ke ganin shi ya kasance mai barazana ga al’umma, wanda kuma ya ke da tarihi na aikata laifi, to a bayyana shi.”

Exit mobile version