Hussaini Baba" />

An Horas Da Jamián Tsaron Fararen Hula 1,050 Kan Tsaron Zabe A Zamfara

Jami’an tsaron fararen hula wato NSCDC, ta bayyana shirya wa ranakun zabe a jihar Zamfara dan ganin an yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sabon Kwamandan na jihar Zamfara, A.A.Garba ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatarwa ‘yan jaridu tsare tsaren ayyukan rundunar su a hedikwatar ta jihar da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Kwamanda ya bayyana cewa “Dakarun su ,1050, suka ba horo dan ganin an samu nasarar gudanar da zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisun dattawa tarayya da na gwamna da na jahohi a fadin mazabu 147, da kuma runfunan zabe 2,516,da muke da ake da su a fadin jihar ta Zamfara. Kuma mun raba Jami’an mu yankuna uku da suka hada da Zamfara ta tsakiya da ta Yamma da kuma ta Arewa dan ganin ba a samu matsalar gudanar da zaben ba.”
“Bugu da kari kuma rundumar mu tana da hadin gwiwa da sauran kungiyoyin tsaro, za mu tabbatar da mun ba da ingantace tsaro, a runfunan da ake gudanar da zabe a duk fadin jihar ta Zamfara.Muna masu tabbatar maku da cewa Rundunar mu ta shirya tsaf dan ganin dakile duk wani yunkuri da zai iya kawo ma zabe cikas a wannan jihar.
“Saboda haka muke kira ga al’ummar jihar Zamfara da su bi ka’idar sharuddan da Hukumar zabe wadanda ta sanya cikin dokokin ta, dan ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana. Muna masu tabbatar maku da cewar wannan lokacin rundunar mu ba za ta saurara ma duk wanda ya nemi ya kawo wata hatsaniya da kuma tashin hankali a runfunan zabe ba,” in ji shi .

Exit mobile version