An Jefar Da Jarirai Biyu Cikin Bola A Ebonyi

Daga Sabo Ahmad,

Rundunar ‘yansandan jihar Ebonyi, ta tabbatar da jefar da wasu jarirai guda biyu cikin bola, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsu.

Jami’ar ‘yansanda mai suna, DSP Lobeth Okworogbuanya, wadda ta je gurin da abin ya faru, ta shaidawa majiyarmu cewa, jariran da aka watsar dukkansu maza ne.

Ta ce, jariri daya an tsince shi ne, a gefen hanyar Kpirikpiri Ogbaga, shi kuma jariri na biyu a Ogbe Hausa.

“Da safe na samu kiran waya daga Shugabar kungiyar lauyoyi mata ta kasa, reshen jihar Ebonyi, Misis Grace, wadda ta gaya min cewa, an tsinci wani jefar da aka jefar !

“Haka kuma ba jimawa, sai ga wani rahoton shi ma da ke cewa, an ga wani mutum wanda ba iya gane shi ba, saboda lokacin dare ne, ya ajiye wani abu a kwali, daga baya aka gane cewa, jariri ne ya jefar, kuma har ma ya mutu.

daya daga cikin jariran da aka jefar, an nade shi ne, aka sa shi a cikin kwali aka jefar da kwalin.

Da ka ga jariran, za ka tabbatar ba su wuce kwana daya ba da haihuwa. Ana cikin wannan sai muka sake samun labarin ga shi can an sake jefar da wani jaririn.

Jami’an ma’aikatar lafiya da ‘yansanda suka debe gawar jariran suka je suka binne su. Okworogbuanya ta bayyana cewa, wannan abin da aka yi tsabar rashin tausayi ne.

A karshe ta ce, za su ci gaba da bincike, har sai sun gano wadanda suka aikata wannan laifin, su gurfanar da su a gaban kotu, don yi musu hukuncin da ya dace.

Exit mobile version