Connect with us

RAHOTANNI

An Jinjina Wa Gwamnatin Kano Bisa Tallafa Wa Mata

Published

on

An Jinjinawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano, wajen taimakawa mata masu karamin karfi, inda aka tallafawa matan da shinkafa, man girki da kuma tufafi domin rage musu radadin zaman gidan da ake yi a halin yanzu.

Jawabin haka, ya fito ne daga bakin Kwamishinan Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad wanda Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Auwal Umar ya wakilta a lokacin kaddamar da rabon tallafin.

Har ila yau, wadanda suka amfana da tallafin akwai Malaman wucin gadi na gidan Marayu da ke Nasarawa.

Alhaji Auwal Umar Sanda ya ce, tallafin ya zama dole idan aka yi la’akari da halin da masu karamin karfi a cikin al’umma ke fuskanta sakamakon wannan cuta ta Korona.

Daga nan, sai ya bukaci al’umma da su rungumi  al’adar wanke hannu da kuma yin amfani da man tsaftace hannu domin dakile yaduwar wannan cuta. Haka kuma, ya bukaci al’umma da su kara himmatuwa wajen gudanar da addu’o’i a cikin wannan wata mai albarka na Azumi.

Haka zalika, Babban Sakataren ya bukaci masu hannu da shuni a cikin al’umma, da su rika bayar da irin wannan gudunmawa domin samun kyakkyawan sakamako a wurin Allah Madaukakin Sarki.

Da su ke gabatar da jawabansu daban-daban, HajiyaA’ishatu Sani Kurawa, Shugabar da ke lura da gidajen nakasassu na Tudun Maliki da kuma Shugabar gidan marayu na Nasarawa, Hajiya Lauriyya sun bayyana farin cikinsu ga Gwamnatin Jihar Kano bisa wannan tagomashi.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi, Malama Kubra da Uwa Andu sun gode wa  Gwamnan Jihar Kano, bisa wannan kayayyakin arziki da ya samar, daga nan sai suka jaddada aniyarsu ta  bayar da dukkanin goyon baya tare da hadin kai ga Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A wani cigaban kuma, Ma’aikatar Mata tare da hadin guiwa da Gidauniyar bayarda da tallafi ta Isa Wali, sun shirya wani taron tattaunawa, domin daukar matakan gaggawa don magance matsalar fyade da kuma tashe-tashen hankula a wannan lokaci da ake fama da annobar cutar Korona, kamar yadda Jami’ar Yada Labaran Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano, Bahijja Malam Kabara ta shaida wa Jaridar LEADERSHIP A YAU.

Advertisement

labarai