Tsofaffin Daliban Makarantar Koyon Harkokin Kasuwanci ta Wudil (WUCOBA) Aji na 1986 sun gudanar da taronsu, kamar yadda suka saba yi, inda shugaban kungiyar, Dr. Rabiu Nana, ya jinjina wa kokarin mambobin kungiyar bisa namijin kokarin da su ke yi wajen halartar irin wannan taro kowace shekara.
Dr. Rabiu Nana a cikin jawabinsa ya bayyana nasarorin da aka cimma cikin Shekarar data gabata, musamman shawarar daga wannan taro zuwa Shekara ta gaba Lokacin da ‘ya’yan kungiyar ke cika shekara 35 da kammala karatu, ziyarar zumunci, Ta’aziyyar ‘yan uwa da aka rasa, sai kuma Mota da dan wannan Kungiya kuma tsohon dalibin WUCOBA, Wakilin al’ummar Dawakin da Warawa a Majalisar wakilai ta Tarayya Alhaji Mustapha Bala Dawaki ya gwangwaje Kungiyar da motar aiki.
Da ya ke gabatar da jawabinsa alokacin taron guda cikin jagororinmu wannan Kungiya Alhaji Suleiman Uba Gaya Wanda Kuma shi ne mataimakin shugaban Kungiyar Editoci na Kasa, shugaban Kamfanin Skylimit wanda ke buga Jaridar jamhuriyy da New Republican ya jinjana shugabannin wannan Kungiyar bisa jajircewar su wajen ganin wannan taro na gudanar yadda yadda kamata.
Haka kuma ya yaba da kokarin Alhaji Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmawar kyautar mota ga wannan Kungiya, yace wannan abin alhairi ne kwarai da gaske, sannan ya bukaci da aka himmatuwa wajen kyautata zumunci a tsakaninmu.
Shi ma a nasa jawabin shugaban makarantar WUCOBA Alhaji Abdallah Utai ya godewa Tsoffin daliban nasa bisa hadin kai da kuma girmamawar da suke masa, saboda haka sai ya yi addu’ar fatan dorewar wannan hadin kai.
Taron ya samu halartar wannan taro akwai tsohon Shugaban makarantar Alhaji Abdallah Utai, Hon. Mustapha Bala Dawaki, Dr. Suleiman Uba Gaya, Alhaji Aminu Aliyu, Alhaji Inusa Abdu Dambazau, Alhaji Auwalu Mu”azu da sauran dalibai ‘yan aji na Shekara ta 1986. Taron da ya gudana a dakin taro na Hukumar yawon bude ido ta Jihar Kano.