Wata kungiyar mai suna ‘Gade Development and Cultural Association,’ wato GDCA ta jinjinawa gwamnan Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bisa zabar kwararru domin ba su mukami a matakai daban-daban a jihar.
A takardar da shugaban kungiyar na kasa ya fitar, Danladi-Ibn Uman, ya ce kungiyarsu ta jinjinawa Gwamnan bisa zabar mutane masu mutunci a cikin tawagar gwamnatinsa. Ya ci gaba da cewa; kungiyar GDCA ta ga hangen nesan gwamnan bisa zabar kwararru a matsayin Kwamishinoninsa da kuma masu ba shi shawarwari da masu taimaka masa.
Sannan har wala yau, GDCA sun taya wadanda aka bai wa mukaman murna, inda suka yi musu addu’ar fatan alheri da kuma kariyar Allah wajen gudanar da ayyukansu.