CRI Hausa" />

An Jinjinawa Kasar Sin Bisa Tallafinta Ga Kasashen Afirka A Fannin Yaki Da Annoba Da Shawo Kan Tashe-tashen Hankula

Shaihun malami a tsangayar ilimin siyasa, kuma daraktan cibiyar nazarin dokoki a jami’ar Abuja ta Najeriya farfesa Sherrif Ghali, ya ce har kullum, Sin a shirye take ta taimakawa kasashen Afirka, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula. Kamar dai yadda Sin din ta nuna hakan, yayin taron kwamitin tsaron MDD na baya bayan nan.

Shaihun malamin ya ce, Sin ta nuna cikakkiyar ’yan uwantakar dake tsakanin ta da kasashen Afirka, a gabar da sassan biyu ke wakilta, da taimakawa juna a mataki na MDD. Don haka Sin ta yi abun da ya dace dukkanin manyan kasashen duniya su yi.
Farfesa Sherrif Ghali ya ce “Muna fatan ganin an aiwatar da hadin gwiwa mai ma’ana tsakanin sassan kasa da kasa, ta yadda hakan zai taimakawa Afirka, wajen shawo kan annoba, da bunkasa farfadowar tattalin arzikin nahiyar, tare da warware kalubalen ci gaba da na tsaro dake addabar ta. (Saminu Hassan)

Exit mobile version