Daga Umar Faruk,
Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin Kwamishinan ma’aikatar kiwon Lafiya kuma shugaban Kwamitin Kula Cutar Korona a Jihar ta Kebbi, Jafar Muhammad ya kaddamar da bikin fara karba alluran Rigakafin Korona a jihar kebbi.
An gudanar da bikin kaddamar da allurar ta riga- kafin ne a dakin gudanar da taro na Asibitin Kwararu ta gwamnatin Jihar Kebbi wato (Kebbi Medical Centre) da ke Kalgo a jiya, Inda aka cif medical Darakta na Kebbi Medical Centre da ke Kalgo, Dakta Abubakar Koko ya zama na farko da karbar allurar ta Rigakafin Korona sai kuma cif medical Darakta kuma sakataren din-din-din na Babbar Asibitin Tunawa da sarki Yahaya, Dakta Aminu Haliru Bunza wanda ya kasance mutun na biyu a duk fadin Jihar da suka karbi allurar Rigakafin Korona a jihar ta Kebbi a jiya.
Yayin kaddamar da allurar Rigakafin Korona a jihar, Kwamishinan ma’aikatar kiwon Lafiya kuma shugaban Kwamitin Kula da Cutar Korona Jafar Muhammad ya bayyana cewa” amada din Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kaddamar da fara bayar da allurar Rigakafin Korona ga al’ummar jihar, amma an fara da ma’aikatar kiwon lafiya ne domin su ne ke Kula da marasa lafiya musamman Cutar Korona, inji Kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya yayin kaddamar da fara bayar da allurar Rigakafin Korona a Jihar Kebbi a jiya”.
Ya ci gaba da cewa” kafin kaddamar da wannan tsarin na bayar da allurar Rigakafin Korona a Jihar ta Kebbi mun gudanar da yekuwa da kuma fadakar wa ga al’ummar jihar ta hannun Sarakunan gargaji da kuma hakimawa na duk fadin Jihar wanda kan ya sanya al’ummar Jihar sun cire tsoro da kuma amincewa da cewa allurar Rigakafin bata da wata illa ga jikin dan’adam, inji Shi.
Haka kuma ya ce, “Idan aka kammala yiwa jami’an kiwon lafiya da sauran ma’aikatar kiwon lafiya zamu sanarwar yan jarida wadanda za a baiwa domin an yi tsari bisa ga rukunin jama’ar da za a baiwa alluran har zuwa ga al’ummar karkara, inji Kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya Jafar Muhammad”.
Daga karshe Kwamishinan Jafar Muhammad ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito su karbi allurar Rigakafin bata da wata matsala domin sai da aka tabbatar da ingancinta kafin aka yadda da a yiwa al’umma ita,