Connect with us

MANYAN LABARAI

An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Harkokin Banki A Kano

Published

on

A farkon makon da ya gabata ne Kamfanin Bizi Mobile tare da hadin gwiwar Babban Bankin Kasa bangarorin da suka shahara wajen tababtar da ci gaban harkokin kudi wanda duniya tuni ta ci gaba a wannan bangare, Kamfanin Bizi Mobile yanzu haka kusan ya karade jihohin kasar nnan ta fuskar samar da hanyoyin masu sauki wajen mu’amilla da kudade wanda duniya tuni ta wuce maganar rungumar tsaba kudin a jaka.

Bikin baje kolin wanda aka gudanar a Fadar mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ya samu halartar kusan daukacin bankunan da suka amsa sunansu ta fuskar hada-hadar kudin a fadin kasar nan.

Haka kuma abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda jama’a suka yi fitar dango wanjen halartar taron domin shiga cikin tsarin wanda idan aka yi sa’a lokaci ya yi da jama’ar mu za a kawo karshen kyamar da suke yi wa harkokin banki.

Da yake gabatar da jawabin yayin kaddamar da shirin na kwana biyar, Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana bukatar jama’ar jihar Kano kasancewarsu cibiyar ciniki da su shiga cikin wannan shiri, musamman ganin yadda makwabtanmu na kudancin kasar nan suka yi nisa wajen shiga cikin wannan tsari, haka kuma ya ambata cewa kasar Ghana da Kenya sun amfana da wannan shirin.

Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce tunanin samar da wannan tsari ya biyo bayan nazarin da masana suka yi wajen lura da hatsarin da ke tattare rungumar tsabar kudi domin gudanar da harkokin kasuwancinsu, saboda haka Sarkin ya jinjina wa shugaban Kamfanin Bizi Mobile, bisa tsayuwar dakan da ya yi tare da hadin gwiwar Babban Bankin kasa.

Alhaji Aminu Aminu Bizi  shi ne shugaban Kamfanin Bizi Mobile ya bayyana dalilin shirya wannan gagarumin taro wanda aka kira da baje kolin harkokin bankuna domin kusantar da su ga jama’a. Ya ce, an tsara gudanar da wannan baje koli na tsawon kwana biyar, saboda haka duk mai bukatar bude asusun ajiya za a yi masa take a wurin a kuma ba shi katin cire kudi a duk inda yake bukata.

Aminu ya ci gaba da cewa muna alfahari da hadin kan da Mai martaba Sarkin Kano ke bai wa wannan shiri, wannan kuma ya ce ya biyo bayan tsananin kishin da sarkin ke dashi na al’ummarsa, don haka sai ya bukaci jama’a a kananan Hukumomin jihar Kano 44, da cewa kowa ya zama cikin shiri domin wannan shiri zai shiga kowace karamar hukuma domin bude wa jama’a asusun ajiya tare da ba su katin cire kudi a duk inda suke.

A karshe, Aminu Bizi ya gode wa shugabar reshen Babban Banki Kasa Hajiya Bilkisu Mashe Wali bisa samun damar halartawa wannan gagarun biki.

Ita ma shugabar reshen Bankin, Hajiya Bilkisu Mashe Wali ta bayyaana cewa Hukumar Babban bankin kasa ta gamsu wa da kokarin Aminu Bizi ta sa ta hada karfi da shi wajen isar da wannan sako, don haka, Hajiya Bilkisu ta jaddada bukatar da ake da ita na ganin jama’ar Kano sun rungumi wannan shiri domin cin gajiyarsa.

Bikin kaddamar da baje kolin ya samu halartar manyan Baki tare da daukacin bankunan da duniyar wannan zamani ke alfahari da su, sai kuma dubundubatar  jama’a daga bangarori daban-daban na al’umma wadanda suka halarci bikin domin ganewa idonsu tare da shiga cikin tsarin.

Haka shugaban Kamfanin Bizi Mobile  ya sanar da cewa  bayan kammala wadannan kwanaki biyar za a shiga kananan hukumomin jihar Kano 44 domin ci gaba da wannan aiki wanda ake fatan kafin nan da wani lokacin kowane dan jihar Kano zai mallaki asusun ajiya a Banki.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: