Yau Alhamis ranar 10 ga wata, an fara “Ranar Sinanci ta MDD” ta shekarar 2025, wato bikin nuna fina-finan Sinanci na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG karo na 5 a hukumance.
An kaddamar da bikin bisa hadin gwiwar CMG da kungiyar wakilan kasar Sin na MDD dake birnin Geneva da na sauran kungiyoyin kasa da kasa, da ofishin MDD dake birnin Geneva. Daga cikin shirye-shiryen bikin mai taken “Ziyara A kasar Sin” wato “China Travel” a Turance, an gayyaci jama’ar kasashen duniya da su tsara bidiyo game da ziyararsu a kasar Sin, inda suka nuna kyawawan al’adu da zamantakewar al’umma na kasar Sin, da kuma yanayin bunkasuwar kasa, domin samar wa al’ummomin damar kara fahimtarsu game da kasar Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)