Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

An Kaddamar Da Gasar Karatun Alkur’ani Karo Na 24 A Zamfara

by Muhammad
January 27, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Karatun
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Hussaini Yero,

Gwamnan jihar Zamfara,Bello Muhammad Matawallen Maradun,ya kadddmar da gasar karatun Alkur’ani,Mai tsarki karo na 24 , wanda aka farashi a ranar litin da ta gabata.

Da ya ke gabatar da jawabinsa a wurin taron,wakilin gwamnan,Sakataren gwamnatin jihar ,Alhaji Bala Bello Maru ya bayyana cewa,’Gwamnati ta kafa Kwamitin gasar karatun Alkur’ani dan karfafa Hukumar kula da Haadda da Tajiwudi ,dan ganin an karanta Alkur’ani kamar yadda Allah ya saukar da shi.kuma gwamnatin na ba da tallafi ga makaranta Alkur’ani, musamman mahaddatta Alkur’ani da makarantun tsangaya dan ganin an habaka ilimin addinin musulunci a cikin jihar.’A jawabin Gwamnan .

Matawallen Maradun ya kara da cewa, “Gwamnatinsa za ta ci gaba da yin biyayya ga duk abin da ya shafi Alkur’ani mai girma da kuma isar da sakonsa da bin koyarwarsa, kuma bukaci alkalan gasar da su kasance masu adalci da tsoron Allah a wajan gudanar da gasar, don fidda hazikai wadanda za su wakilci jihar a gasa ta kasa da za a gabatar a Jihar Kano, babban fatanmu shine Jihar Zamfara ta zamo na daya a matakin Kasa da za ta wakilci Nijeriya a gasar ta Duniya.”

Ya kuma bukakaci a rinka karrama masu haddar karatun AlKur’ani, tare da sanyasu su rinka bita ga limaman masallatai, ya Kuma nemi masu gasar dasu kasance masu Jin tsoron Allah madaukakin sarki a duk inda suke.

Shugaban Kwamitin gasar na Jihar Zamfara,Alhaji Ibrahim Ruwan Dorawa ya tabbatar da cewa, za su yi iyakokarin su na ganin sunfida hazikan dalibai da zasu samu nasara a matakin kasa da wajenta.

Don ganin kudn basu kawo ma gasar cikas ba, Shugaban Kwamitin gasar Alhaji Ibrahim Ruwan Dorawa ya ba Kwamitin gudunmuwar naira miliyan goma,dan samun nasara gasar.

A karshe sakataren zartarwa na Hukumar Haadda da Tajiwudi na jihar, Malam Hadi Suleman Modibon Gusau, ya bayyana godiya sa ga Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamnan Bello Matawallen Maradun akan gudunmuwar da suke ba Hukumar da kuma Shugaban Kwamitin gasar Alhaji Ibrahim Ruwan Dorawa da ya zamo uba akan tafiyar da Kwamitin ya bada dukiyar sa da jikinsa dan samun nasarar wanna gasa.

Malam Hadi Suleman ya kuma tabbatar da cewa, alkalai za su yi iya kokarinsu wajen fidda zakaru da za su kara a matakin kasa kuma su wakilci Nigeria a gasar ta duniya kuma mu samo nasara kamar yadda muka Saba da yardar Allah, in ji Sakataren Modibon Gusau, Hadi Suleman.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kungiyar ‘Love Your Neighbour’ Ta Karrama Shugaban Karamar Hukumar Lokoja

Next Post

NAF Ta Karfafa Kawancenta Da Kasar Hungary Don Yakar Ta’addanci A Nijeriya

RelatedPosts

APC

APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbin Dan Majalisa A Jigawa 

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Munkaila Abdullah, Hukumar zabe ta INEC ta bayyana Jam'iyya...

Masar

Ilimi: Jakadan Kasar Masar a Nijeriya Ya Yi Alkawarin Hada Hannu Da Gwamnatin Kano

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Jakadan Kasar Egypt a Nijeriya ya...

Suleja

Mun Gamsu Da Ayyukan Dan Majalisar Wakilai Na Suleja – Inijinya Kabiru

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, An bayyana cewar irin rawar da...

Next Post
NAF

NAF Ta Karfafa Kawancenta Da Kasar Hungary Don Yakar Ta'addanci A Nijeriya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version