An kaddamar da Kungiyar Cigaban Al’umma ta ‘Battlers’ da ta hada unguwannin Zage, Dorayi, Zango tare da aza harsashin ginin ofishinta da bada tallafin kayan aiki ga makarantu da kayan sawa ga daliban makarantu.
Taron, wanda ya gudanane a filin karofin Zage a ranar Asabar, da ya ke jawabi Shugaban Karamar hukumar Birnin Kano Hon.Sabo Dantata wanda Kansilar Mazabar Zango Hon.Gambo Muhammad ya wakilta ya bayyana mutukar farin cikinsa bisa irin kokari da kungiyar take wajen bunkasa cigaban al’ummar a matsayinsa na Kansilan yankin.
Ya ce kokarin kungiyar na dakile shaye-shayen kwayoyi da daba ya kawo saukin miyagun ayyuka a yankin haka kuma kokarinsu na habaka cigaban ilimi.
Ya ce Karamar hukumar Birni kamar sauran Kananan hukumomin Kano ta karbo bashin kudi domin habaka shirinda Gwamnatin Kano ta bullo dashi na ilimi kyauta kuma wajibi dan amfanar al’umma, dan haka yakamata al’umma, musamman iyaye da malamai su rika taimakawa shirin ta yin aiki tukuru da kuma tura yara makaranta.
Hon. Gambo Muhammad Kofar Mata ya ce duk wani abu na taimakawa cigaban kungiyar a matakin karamar hukumar zai cigaba da wucewa gaba dan tabbatar dashi musamman ma bukatunsu da suka gabatar masa tun a baya cikin dan lokaci zai tabbata.
Tun a farko a jawabinsa Shugaban kungiyar na “BATTLERS” Alhaji Salisu Ibrahim Zage ya ce, wannan taro an shiryane dan kaddamar da kungiyar a hukumance da kuma sanya harsashin gina ofishinta. Dama burin kungiyar shine kawo gyara ga matasa ta hana shaye-shaye da fadace-fadacen daba,idan aka kauda wannan sai a dorasu akan koyon sana’oi da neman ilimi ta sasu a makarantu su sami ilimi dan gina cigabansu dana al’umma.
Ya ce, idan aka kyalesu a cikin miyagun hali al’umma ta lalace idan a ka raya su akan kyawawan dabi’u al’umma za ta rayu a samu baya mai inganci, su sami ilimi da cigaba a rayuwa musamman a tsakanin unguwanninsu.
Ya yi nuni da cewa an kafa kungiyar a cikin 2018. Kafin kafata in aka ce zage da kewayen unguwanni da suke a wajen saika zaci yan daba ne kawai, amma zuwan kungiyar komai ya daidaita domin duk masu aikata laifin an kama yawancinsu, wasu sun gyara halayensu wasu sun gudu,yanzu Unguwanin Zango da Zage sa Dorayi sun zama abin kwatance har ana misali dasu,saboda sun fito gaba daya ba sani ba sabo sun hada kai sun gyara unguwanninsu.
Ya ce su na godiya ga Allah yanzu unguwannin sunyi lafiya.Yace da a farko sun sami matsala na rashin fahimta daga masu aikata abinda bai kamata ba, amma daga baya sun gane gata ake mu su wajen a gyara tarbiyarsu,yanzu sunzo ma ana tafiya tare dasu.
Alhaji Salisu Ibrahim Zage ya ce burinsu a kan kungiyar su ga ta bunkasa ta zana abin dogaro ga matasa wajen yin karatu da samun aikinyi sunaso suga Yara sun zama lafiyayyu ba shaye-shaye da daba su zama mutane nagari.Wannan kuwa ana bukatar mutane suzo su bada goyon baya kuma suna zuwa, su na bayarwa domin kowa akwai bukatar ya sa hannu ya taimaka wa kungiya in a ka bar su su kadai, za su gaza amma in aka hadu har da hukuma za a cigaba da samun nasarar abinda a ka sa a gaba.
A lokacin taron an kaddamarda Kalandan kungiyar tareda tallafawa masu gudanarda aikin hakar kabari na yankin. Sannan an karrama dinbin mutane da su ke bada gudummuwa ga cigaban kungiyar.
Daga cikin wadanda su ka halarci taron sun hada da Alhaji Habibu Dukawa da Tsohon Minista Musa Barodo da Sheik Ibrahim Khalil da dinbin al’ummar unguwannin yankin.