An Kaddamar Da Manhajar Saye Da Sayarwa Ta Intanet

Cibiyar hada-hadar kasuwanci ta zamani ta n kaddamar da hada-hadar kasuwanci ta duniya ta zamani wato (global e-commerce platform, Mall For Africa), ta sanar da kokarin da take yi na taimaka wa matsakaitan sana’oin dake akeyi a kasar nan yadda zasu kasance masu tsayawa da kafafunsu don kara ciyar da tattalin arkinbkasar nan gaba. Acewar MFA, sabon kayan da a turance ake kira Concierge BIP Serbices,an sanya shine don cimma buatun kasuwanci na dukkan masu hannu da shuni

na sauran alumma da kuma Kamfanoni wadanda basu da lokacin sayen kayan da suke da bukata. A lokacin da aka kaddamar da kayan Shugaban MFA na nahiyar Afirka Kwame Acheampong  ya ce, masu matsakaitan sana’oin zasu iya yin baje kolin sana’oinsu ta kafar. Ya kara da cewar, muna kuma da wasu kayan da ake kira samar da kasuwa a Afirka, inda masu matsakaitan sana’oin zasu dinga fitar da kayansu zuwa kasashen waje. Ya ce, mune masu sanyawa a fitar da kayan zuwa kasar waje kuma muna tunkaho mu yan Afirka ne kuma luna son mu taimaki yan Afirka. Ya bayyana cewar, a kanmaganar fitar da kaya waje na matsakaitan sana’oin kamar na zanen kaya da sauran su zamu iya yin hanya don a kai kayan ksar waje. Ya ce, wannnan shine karo na farko da wani zai iya kai kayan sa zuwa kasar waje.

Exit mobile version