Daga Abubakar Abba
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya kaddamar da rumbun adana Doya na zamani a jami’ar koyon darrisan aikin noma ta Keffi-Shabu- Lafia dake a jihar Nasarawa.
A cewar Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono, rumbun zai iya adana daga tan 45 zuwa tan 50 na Doya kuma Ana san za a iya samun Irin na Doya da za a iya shuka wa a kadada 16.
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya bayyana hakan ne a jawabinsa a yayin kaddamarwar a makon da ya gabata.
Ministan Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa yin amfani da ingantacce Irin noman Doya zai taimaka matuka wajen kara samar da kudaden shiga masu yawa ga manoman Doya da kuma kara habaka fannin a jihar ta Nasarawa harda Doyar da aka fitar zuwa kasuwannin duniya .
A cewar Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono, gudanar da aikin a jami’ar zai taimaka matuka wajen kara gudanar da bincike, ilimantar wa, kara samar wa da manoma da kudade shiga masu yawa inda kuma aikin, zai kara samar da ayyukan yi kimanin 200.
“Gudanar da aikin a cikin wannan jami’ar zai taimaka matuka wajen kara gudanar da bincike, ilimantar wa, kara samar wa da manoma da kudade shiga masu yawa inda kuma aikin, zai kara samar da ayyukan yi kimanin 200.”
Shi ma a na sa jawabin a gurin taron taron, Shugaban Jami’ar jihar Nasarawa Farfesa Suleiman Mohammed ya sanar da cewa, za a yi amfani da Rumbun yadda ya da ce, musamman domin a karfafa kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi na daukaka gudanar da bincike kan fannin da kuma kara habaka fannin tattalin arzikin kasar.
A cewar Shugaban Jami’ar jihar Nasarawa Farfesa Suleiman Mohammed, gwamnatin jihar Nasarawa ya fitar da naira miliyan 35 domin kara inganta samar da ingantacce Irin na Doya a jihar.
“Za a yi amfani da Rumbun yadda ya da ce, musamman domin a karfafa kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi na daukaka gudanar da bincike kan fannin da kuma kara habaka fannin tattalin arzikin kasar.Bugu da karin, Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono a wani aikin kuma tare da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa na aikin gona Sanata Abdullahi Adamu, sun kai ziyarar aiki a wata gona ta zamani ta Shabu dake a karamar hukumar Kokona a cikin jihar ta Nasarawa.”
A yayin wannan ziyarar ta su, sun kuma nuna jin dadinsu kan samar da Rumbunan zamani na adana Doya da kungiyar kasa da kasa ta RIELA ta samar a gonar tare da kuma samar sa kayan aikin gona a jihar Nasarawa.
Har ila yau, Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono, an kuma zagaya dashi wasu guraren da ake gudanar da aikin noma a jihar Nasarawa.
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkar Alhaji Muhammad Sabo Nanono tare da Gwamnan jihar Nassarawa Abdulahi Sule a tun da farko, sun kai wata ziyarar aiki a gonar Sukari ta dangote mai fadin kadada 68,000 sake a yankin Tunga a jihar Nassarawa .