Isa Abdullahi Gidan Bakko" />

An Kaddamar Da Shugabannin Kungiyar ’Yan Katako A Sabon Garin Zariya

Kungiyar ’Yan Katako

A makon jiya ne aka kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar ‘yan katako reshen babbar kasuwar ‘yan katako da Sabon garin Zariya, da taron kaddamar da sabbin shugabannin ya sami halartar wakilan shugabannin ‘yan kasuwar Sabon gari da manya da kuma kananan ‘yan kasuwa da suka fito daga sassan Jihar Kaduna.

Sabbin shugabannin da aka zaba sun hada da kujerar shugaban kungiyar aka zabi tsohon matakin shugaban kungiyar Alhaji Suleiman Yusuf, wanda aka fi sani da sunan na Hari, mai Allah, sai matakin shugaba aka zabi Alhaji Lawal Garba sai babban sakataren kungiyar aka zabi Muhammed Gali sai kujerar ma’ajin kungiyar, aka zabi Alhaji Shehu Ahmed da aka fi sani da magani, sai sakataren kudi, aka zabi BilyaminiSani sai kuma sakataren tysare – tsaren kungiyar aka zabi Alhaji Ibrahi Ahmed.

Sauran shugabannin kungiyar da aka zaba sun hada da Alhaji Shehu Hassan Baba, a matsayin jami’in watsa labarai na kungiyar, sai jami’in walwala aka zabi Jabir Hassan, sai Yusuf Yunusa a matsayin jami’in watsa labarai, sai babban jami’in watsa labarai da aka zabi, Malam Musa Yakubu, sai jami’in ladabtarwa aka zabi, Alhaji Aliyu Abdullahi, sai mai shari’a a wannan kungiyar aka zabi Alhaji Salisu Mhammed da kuma Alhaji Mohmud Garba Hasan aka zabe shi a kujerar babban jami’in kula da lafiyar shugabanni da kuma sauran ‘ya’yan kungiya, aka zabiAlhaji Mohammed Garba.

A dai lokacin kaddamar da shugannin an zabiAlhaji Aminu Abdullahi a matsayin Jami’in tsaro na wannan kungiya sai mai binciken lalitar kungiyar aka zabi Alhaji Haliru Baba.

A sakonsa wajen kadddamar da sabbin shugabannin, shugaban karamar hukumar Sabon Gari Injiniya Mohammed Usman, ya yaba wa ‘ya’yan kungiyar na yadda suka hada kan su, suka yi wannan zabe, inda aka fara lafiya aka kuma kammala taron lafiya.

Injiniya Mohammed Usman da kansila a wannan karmar hukuma Alhaji Yakubu Furodusa ya wwakilce a wajen taron, ya kira ga sabbin shugabannin da aka kaddanar da su kasance ma su tunanin wadanda suka zabe su, musamman ta tsara wasu hanyoyin da za su aiwatar mambobin kungiyar su amfana ta hanyoyin sana’arsu da kuma iyalansu.

Alhaji Uwaisu wanda ya wakiulci shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na babbar kasuwar Sabon gari, Alhaji Ibrahim mai gwal, shi ma ya nuna matukar jin dadinsa na yadda kafintoci suka hada kansu tare da kafa wannan kungiyar, a cewarsa, babbr kungiyar ‘yan kasuwa ta karamar hukumar Sabon gari, bisa jagoranci Alhaji Ibrahim mai gwal, su na shirye ako wane lokaci, na ganin sun bayar da gudunmuwar day a dace ga mambobin wannan kungiyar, ta yadda mambobin za su furta cewar, sun yi murna da zaben Nahari Mai Allah, a matsayin shugaban kafintoci a sabon gari.

Shi ma jawabinsa, sabon shugaban kungiyar da aka kaddamar a wannan rana Alhaji Suleiman Yusuf, wanda aka fi kira da Na Hari Mai Akllah, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda mambobin kungiyar suka ga dacewarsa ya zama shugaban wannan kungiya, bayan ya yi mataimakin shugaban kungiyar a shekarun baya.

Alhaji Yusuf Na Hari ya lashi takobin duk abin day a dac e kuma dokar kungiyar ta amince, domin ci gaban wannan kungiya ta kafintoci, ta yadda kuma mambobin kungiyar za su amfana da shugabancin da za a yi ma sun an da shekara hudu ma su zuwa.

Da kuma ya juya ga wadanda suka taka rawar gaban hantsi a lokacin zabubbukan da aka yi, amma ba su sami nasara ba, a nan ya sifanta su da cewar, babu abin da ke zukatansu, sai neman damar da za su hau madafun ikon da za su tallafa wa wannan kungiyar da kuma mambobin ta, ya kara da cewar, sun dab a su kai ga samun nasara ba, ya ce ya na fatan za su ba shi duk goyon baya da kuma kyawawan shawarwarin da za su tallafa wa shugabancin kungiyar da kuma mambobinta.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Alhaji Abbas Tanko da Alhaji Uwaisu da kuma tsohon shugaban wannan kungiya, Alhaji Ahmed Isa Goro, inda dukkansu suka lashi takobin ci gaba da rungumar sabbin shugabannin da aka kaddamar da hannu biyu, domin su sami nasarar da ake sa wa gaba da ya shafi cigaban sana’ar kafinta da kuma mabobin kungiyar bakidaya.

Exit mobile version