A yau Litinin 9 ga wata ne memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, da jami’an bangaren Amurka, suka halarci taron farko na tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka, wanda aka kaddamar a birnin London dake kasar Birtaniya. (Zainab Zhang)