Abdullahi Muhammad Sheka" />

An Kaddamar Gasar Cin Kofin Ramat Karo 37 A Kano

An kaddamar da Gasar Cin Kofin Ramat karo 37, wanda Hukumar shirya wasanni ta Matasan Nijeriya (YSFON) ke shirywa a duk shekara, ranar Alhamis da ta gabata a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari a Kano.

Da yake kaddamar da bude wasan, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Wasanni na Matasa na kasa baki-daya ya bayyana cewa, gasar tun a lokacin da aka fara gudanar da ita ta samar da gogaggun ‘yan wasa a matakai daban-daban a wasannin kwallon kafa a duniya, kamar yadda Daraktan Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Lahadi.

Mataimakin Gwamnan, wanda Kwamishinan Wasanni, Alhaji Ibrahim Galadima ya wakilta ya jaddada aniyar Gwamnatin Ganduje, na ciyar da harkar wasanni gaba musamman wadanda ke yi matakin farko na kasa da kasa.

“Za mu cigaba da bayar da cikakken goyon baya ga cigaban gasar wasannin kwallon kananan Matasa, domin samar da kwararru a tsakanin Matasan.”

Daga nan sai ya jinjinawa YSFON, bisa cigaban da aka samu wajen shirya irin wannan wasa a tsawon shekaru goma, wanda Jihar Kano ke daukar nauyin wasan.

Da yake gabatar da nasa jawabin, Sakataren Kungiyar ta YOSFAN na kasa, Mista Patrick Okpabuerhe cewa ya yi, kungiyoyi daga jihohi 36 har da Abuja ne suka shiga cikin wannan gasa.

Ya kara da cewa, babban dalilin YOFAN na shirya irin wadannan wasanni shi ne, domin shigo da Matasa cikin gasar cin kofin na Ramat ‘yan kasa da shekaru 16, wadanda ake fatan su zama taurari a wannan kasa nan gaba kadan.

Wasan da aka fara bude gasar da shi su ne, kungiyar Kano wanda kuma su ne ke rike da kambun, sannan kungiyar Kwara ta yi kan-kan-kan da takwararta daga Kaduna.

Exit mobile version