Mustapha Ibrahim" />

An Kafa Makarantar Kitmer Don Samar Da Likitoci A Kowanne Gida Ta Magungunan Gargajiya – Dakta Kachako

Babban burin da ya sa a ka kafa makarantar horar da matasa, maza da mata har da matan aure da dattawa da daukacin al’umma su kware kuma su san hakikanin Ilimi na kiwon lafiya gaba-gaba na Jikin Dan Adam gabadayansa dan haka a kafa wannan cibiya ta ilimantarwa da bincike akan fanin Magugunan Gargajiya ta yadda kowanne Gida za’a iyya samun a kalla mace daya zata iya bada magani a kalla na taimakon farko, shi ne makasudin kafa Kimec Institude for Traditional Medicine And Resources (KITMER).

Wannan  bayanin ya fito ne daga bakin Dakta Yakubu Mai Gida Kachako shugaban Makarantar Horar da al’umma ilimumukan magugunan gargajiya ta hanyar zamani a lokacin da yake Jawabi a wani taro na Tautaunawa da Daliban Makarantar a gaban al’umma masana na zamani da kuma masana akan ilimumukan gargajiya wanda aka gabatar a wannan lokaci a taron da aka yiwa lakabi da Maraba da Ramadan wanda Dalibai suka bajakolin fasaharsu ta hanyar bayani dala-dala akan halittun Dan Adam da kuma amfanin su kamar kwakwalwa da mahaifa, hanta, saifa, koda, zuciya da sauran su wanda shehunan Malamai suka halarta kamar su Farfesa Musa Alhaji, Shugaban Jami’ar Wudil, da kuma Farfesa Rabi’u Magaji Kwarare masanin Kwakwalwa da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ABUwanda yagabata a  birnin kano.

A jawabin Dakta Kachako yace ganin yadda kasashe irin su chaina, Misira, India, Japan, da sauransu su kayi nisa wajen sani da bincike akan ilimin Magungunan Gargajiya kuma suke cin gajiyar sa shi ya sa aka kafa KITMER, domin Ilimantar da mutanan mu wanda sukayi karatun zamani da ma wanda basu yiba, wannan ilimi domin  amfanin mu a al’ummar mu musamman mu Nijeriya da Allah ya hore mana albarkatun Ganyeyyaki da tsire-tsire da sauran albarka da Allah yaba kasar nan. 

Haka kuma yayi kira da Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan su tallafama irin wadannan makarantu domin za su rag e matsalolin lafiya tundaga gida za’a iya tsayarda Cututtuka masu yawa ta hanyar wannan Ilimi inda ya baiyyana matsalar da suke fuskanta ta rashin muhalli da rashin kayan aiki wanda suke bukatar Gwamnati ta Kano ta lura da wadannan Abubuwa wanda yace idan da ace Gwamnatin Kano zata dau nauyin mutun biyar-biyar daka ku wacce karamar hukuma su 44 da anga sauyi cikin gaggawa wanda mu yanzu burin mu kowanne gida su zamana a kalla akwai mai ilimin taimakon farko a kowanne fanni na jikin Mutun ta hanyar ilimin Gargajiya. 

Shi ma ferfesa Rabi’u Magaji daga ABU Zariya masanin kwakwalwa da ferfesa Musa Alhaji shugaban Jami’ar kimiya da fasaha ta Wudil KUST sun nuna gamsuwar su da kafa wannan makaranta mai hadin gwiwa da Jami’ar Wudil, Kano.

Exit mobile version