Abba Ibrahim Wada" />

An Kai Ruwa Rana Tsakanin Nijeriya Da Brazil

Kungiyar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles ta rike wa ta Brazil wuya a wasan sada zumunta da su ka buga a filin wasa na ‘The National Stadium’ na kasar Singapore, inda wasa ya tashi 1-1.

A iya cewa kungiyar ta Super Eagles da kyar ta sha domin kuwa Brazil ta fi ta taka kusan kowacce irin rawa a wasan sai dai itama Nigeriya ta kai wasu munanan hare-hare wadanda zata iya zura kwallo a raga.

Najeriya ce ta fara jefa kwallo a raga ta hannun Joe Aribo a minti na 35, inda ya kutsa kai tsakiyar ‘yan bayan Brazil bayan Simon ya ba shi kwallon a cikin yadi na 18, sannan sai dai ya yanke mutum biyu kafin ya tsula ta cikin raga.

Casemiro ne ya farke wa Brazil tata kwallon a minti na 48 bayan kwallon da Markuinhos ya saka wa kai ta bugo turke ta dawo, inda shi kuma Casemiro ya yi azama ya buga ta cikin raga kafin mai tsaron ragar Nigeria ya ankara.

A minti na 12 ne tauraron dan wasa Neymar ya fita daga fili yana dingishi bisa raunin da ya sha fama da shi a gwiwarsa, inda Coutinho ya karbe shi ciwon da a ke ganin ba zai yiwa dan wasan da kungiyarsa dadi ba.

Da Neymar ya ci kwallo a yau din da ya kamo Ronaldo a matsayin dan wasa na biyu da ya fi zura kwallaye a raga a tawagar ta Brazil – yanzu Pele ne kan gaba da kwallo 77, Ronaldo 62 sai Neymar mai 61.

Wasa na uku kenan a jere da Brazil ta buga ba tare da nasara ba biyo bayan kashin da ta sha a wasannin sada zumunta a hannun kasar Peru da ci 0-1 da kuma canjaras tsakaninta da Colombia duka a watan Satumba.

Ita kuwa Najeriya wasanta na farko ta buga kenan tun bayan nasarar da ta samu a kan Tunisia da ci 1-0 a wasan neman na uku a gasar cin Kofin kasashen Afirka na 2019 wanda kasar Masar ta dauki bakunci.

Exit mobile version