Abba Ibrahim Wada" />

An Kai Wa Dan Wasan Laberiya Hari Saboda Zubar Da Fanareti

Bayan kasa zura kwallo da ya yi a raga a wasan da kasarsa ta fafata da kasar Liberia, wasu matasa sun je gidan dan wasa Umaru Bangura, inda su ka farfasa ma sa gilashin gidan da ke babban birnin kasar Sierra Leone, wato Freetown.

Kasar Sierra Leone dai tana bukatar ta samu nasara a wasan data fafata da kasar ta Liberia domin samun gurbin cancantar shiga gasar cin kofin duniya wanda za’ayi a kasar Katar a shekara ta 2022 mai zuwa. Sierra Leone dai ta na bukatar zura kwallo biyu a raga a wasan nasu domin samun cancantar shiga cikin rukuni kuma a minti na 55 dan wasan gaba na kasar Kei Kamara ya zura kwallon farko yayin da aminti na 90 su ka samu bugun fanareti, amma sai Bangura ya kasa zura kwallon a raga.

Sai dai bayan an tashi daga fafatawar, magoya bayan tawagar kasar sunji haushin yadda sakamakon wasan ya kasance, inda kuma kai tsaye su ka nufi gidan Bangura suka faffasa gilashin gidan da duwatsu sannan kuma suka balla wasu kofofin gidan kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

“Wannan ita ce rana mafi muni a rayuwa ta domin ban taba zaton magoya baya za su iya yimin wannan abun ba, saboda kwallon kafa ce komai ya na iya kasancewa sannan a matsayina na kaftin nayi aikina na zuwa in buga kwallon sai dai ban samu nasara ba saboda haka ina bayar da hakuri” in ji

Bangura Sai dai shima ministan wasannin kasar Ibrahim Nyelenkeh ya bayyana cewa halayyar da magoya baya suka nuna bai da ce ba kuma za suyi bincike domin gano wadanda suka aikata wannan laifi saboda a hukunta su.

A karshe kuma ya bayyana cewa nuna halin rashin da’a a kwallon kafa bai kamata ba ga magoya baya saboda kwallon kafa kasa ne kuma kowa yana iya samun nasara ko rashin nasara saboda haka dole duk mai kallon kwallo sai ya amince da hakan.

Exit mobile version