An kama wata amarya mai suna Saudat a Jihar Kano bisa zargin kashe mijinta, Salisu, bayan kwana tara kacal da aurensu.
Lamarin ya faru ne da daren Litinin a unguwar Farawa, kwanaki kaɗan bayan da aka ɗaura aurensu a ranar Lahadi, 27 ga watan Afrilu, 2025.
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu
- EFCC Ta Kama Matashi A Kaduna Bisa Zargin Wulaƙanta Naira A Bidiyon Barkwanci
Rahoton wani gidan rediyo da wakilinmu ya saurara ya nuna cewar dangin ma’auratan ne suka haɗa auren, amma babu soyayya tsakanin Saudat da Salisu.
An ce Salisu ya ƙi amincewa ds auren tun da farko, amma iyayensa suka shawo kansa ya haƙura aka yi auren.
Kodayake ba a bayyana cikakken yadda lamarin ya faru ba, wasu mazauna yankin sun zargi Saudat da yunƙurin zubanwa mijin nata guba, kafin daga bisani ta daɓa masa wuƙa a lokacin da rikici ya ɓarke a tsakaninsu.
Lamarin ya tayar da hankali a unguwar, inda wasu matasa suka yi yunƙurin kai farmakar Saudat.
Amma jami’an tsaro sun isa wajen a kan lokaci, suka ceci amaryar tare da kai ta wajen hukuma.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.