Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta gano motar Toyota Hilux da aka sace a gidan gwamnatin jihar a ofishin mataimakin gwamna tare da kama wanda ake zargi da satar.
A cewar wani rahoton ‘yansanda, an gano motar ne a safiyar Laraba bayan kaddamar da wani binciken gaggawa da jami’an tsaron suka yi.
- Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu
- Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
An kama wanda ake zargin, wanda aka ce direba ne a ofishin mataimakin gwamna, kuma a halin yanzu yana hannun rundunar tsaro domin ci gaba da amsa tambayoyi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”
“Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar.














