Connect with us

LABARAI

An Kama Masu Gadi Da Laifin Satar Naira Miliyan 5 A Maiduguri

Published

on

Jami’an ‘yan sanda daga sashen masu yakar fashi da makami a Jihar Borno, sun kama wasu masu gadi biyu a bisa zargin su da satar Naira milyan 5 a wani asibitin kwararru na Maiduguri.
Wata tabbatacciyar majiya ta shaida wa manema labarai cewa, an kama masu gadin biyu ne ranar Asabar bayan da aka sami labarin sirri a kan laifin da suka aikata.
Majiyar ta ce, tun a watan Mayu ne jami’an ‘yan sanda suke neman su.
An yi zargin cewa, wadanda ake tuhuman sun saci kudin ne a ranar 1 ga watan Mayu, bayan da suka fasa asusun akawun asibitin, bayan da suka kurda ofishin na shi ta silin.
“Sun sayi mota karama kirar Honda a kan Naira milyan 2.6, sai suka gudu zuwa Kano, inda suka yi ta bindiga da sauran kudin. da suka tsiyace ne sai itama motar suka sayar da ita, nan ma suka kashe kudin na ta, sai suka sake dawowa Maiduguri, a tsiyacen su,” in ji majiyar tamu.
Babban daraktan asibitin, Dakta Laraba Bello, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa, wadanda ake tuhuman masu gadi ne na wani kamfanin masu aikin gadi da aka kawo su gadi a asibitin.
Bello ta ce, “A ranar 1 ga watan Mayu, babban akawun asibitin namu sai ya taras da asusun ajiyar kudin ofishinsa a bude, alhalin kuma ga kofa da taga duk a kulle. Ta silin ne suka shiga ofishin na shi suka sace kudin da ke cikin asusun.”
Ta bayyana cewa, satan ta jefa ma’aikatan asibitin cikin mawuyacin hali da razani.
Da yake bayani, tsohon shugaban kamfanin da ya dauki masu gadin aiki, Mista Babatunde Satomey, mai kamfanin gadi na, ‘HIM Global Nigerian Security Limited,’ cewa ya yi, kamfanin na shi ya kori masu gadin daga aiki ne tun a watan Afrilu, kafin su kai ga aikata wannan laifin.
“Duk korarrun ma’aikata ne a kamfanin mu. [ayansu dai ya yi laifi ne a wurin da muka ajiye shi na karshe, sai muka kore shi, dayan kuma ya kasa aikin da muka sanya shi ne, shi ma sai muka kore shi,” in ji shi.
Satomey ya ce, a baya masu gadin sun biyo wasu ‘yan basukan kudade na ‘yan wasu watanni, amma duk mun biya su.
“Sam ba gaskiya ne ba cewan wai ba mu biya ma’aikatanmu ba har na tsawon watanni takwas. Duk wanda ya shaida maku hakan, karya yake yi,” in ji shi.
Advertisement

labarai