Yusuf Shuaibu" />

An Kama Matasa Biyu Su Na Luwadi

Kashe

Mazauna kauyen Agwete da ke birnin Kakamega na kasar Kenya sun lakadawa wasu matasa biyu mugun duka bayan sun kama su suna luwadi. Kamar yadda jama’ar yankin suka tabbatar, Wani mai suna Wayenso, daya daga cikin matasan da ake zargi da aikata laifin, sun tabbatar da cewa ya saba lalata yaran jama’a.

Shugaban ‘yan sandan yankin ya bayyana cewa, sun ceci matasan inda suka adana su a ofishinsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan lamarin. An bayyana cewa, mazauna kauyen Agwete da ke garin Kakamega na kasar Kenya da sanyin safiya suka kama wadannan matasa biyu a yayin da suke luwadin. Shugaban kungiyar dattawan yankin mai suna Nyumbi Kumi, Reuben Otiende, ya bayyana cewa sun dade suna zargin daya daga cikin matasan mai suna Wanyeso Alias Gili, da zama dan luwadin. An taba kama shi yayin da ya lalata wani yaron makwabcinsu, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Mazaunan yankin sun balle kofar Wanyeso bayan sun ga wani matashi wanda ba dan yankin ba mai suna Caleb Andani, ya shiga gidansa. An kama matasan biyu dumu-dumu yayin da suke aikata wannan mummunan aiki, kuma jama’ar yankin sun lakada musu mugun duka kafin zuwan ‘yan sanda.

K2TB ta ruwaito cewa, Wanyeso Gwauro ne wanda ya saki matarsa mai suna Grace Khabesta a shekarar da ta gabata. Allah ya albarkaci auren nasu da ‘ya’ya uku kafin daga bisani su rabu. Wani makocinsa ya ce, “Wanyeso ya saki matarsa ne ta yadda zai ci karensa babu babbaka ta hanyar yin wannan mummunar harka da ya saba.”

Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna kira ga mai gidan hayar da Wanyeso yake ciki da ya fattake shi saboda ba za mu ci gaba da zama da mai wannan harkar a yankinmu ba. Wadannan ne mutanen da ke lalata mana yara.” Shugaban ‘yan sandan Kakamega ta tsakiya, Dabid Kabena, ya bayyana cewa wadanda ake zargin za a gurfanar da su bayan an kammala bincike. Ba yau matsalar luwadi ke addabar al’umma ba. A kwanakin baya ma an kama wani mutum wanda ake zargi da lalata yara 12 a jihar Sokoto.

Exit mobile version