Daga Sulaiman Ibrahim
“An kama wani jami’in soja da budurwarsa kwanan nan da suke taimaka wa ’yan ta’adda da kakin soji.”
Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Bello Muhammad Matawalle, Dokta Bashir Muhammad Maru, ya shaida wa manema labarai hakan a wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa an samu nasarar kama sojan ne ta hanyar bayanan sirri daga al’umma.
“Yayin da Gwamnatin Jihar ke jiran matakin da Sojoji za su dauka a kan wannan lamarin tare da yin bayani a hukumance, wannan nasarar ta kara tabbatar da ra’ayin Gwamna Bello Mohammed cewa matukar ba ayi maganin masu yiwa gwamnati zagon kasa ba game da yaki da ‘yan ta’adda, to ba za mu iya samun nasarar da ake so asamu a cikin yakin ba.
“Bari in yi amfani da wannan damar don jinjina wa jajirtattun nan masu kishin kasa da suka bamu wannan rahoton da yakaimu ga nasarar cafke wadannan mayaudaran, ”inji shi.
Ko da yake, kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji a jihar Zamfara Kyaftin Ibrahim Yahaya ya ce a yanzu wannan bincike ya zama abin zargi har sai sakamakon binciken da sojojin suka yi ya fito.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta tuntube su ba kafin ta fitar da sanarwar ga manema labarai.