Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Kama Talakan Da Ya Yi Barazanar Kashe Buhari Da Gwamnan Gombe

Published

on

  • Laifin Tsananin Da Na Tsinci Kaina Ne, In Ji Shi

Wani matashi mai shekaru 30 da haihuwa dan kabilar Fulani da ya ke da mata da ‘ya’ya uku mai suna Usman Muhammad dan asalin garin Bambam a karamar hukumar Balanga ta jihar Gombe ya shiga hannu ’yan bijilante sakamakon sawa da ya yi a ka dauki hoton bidiyonsa ya na barazanar kisa ga Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Yayin da wakilin LEADERSHIP A YAU ya ke zantawa da shi, ya bayyana cewa, fitowa ya yi a kafar sada zumunta ya na cewa, idan sun kai su 1,000 irinsu za su hadu su yi gunduwa-gunduwa da Shugban kasa Muhammad Buhari da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Usman Muhammad ya ce, ya furta hakan ne, saboda ya na fama bakin talauci, kuma ya na son gwamnati ta kula da shi, don ya samu yadda zai yi da rayuwa. Ya ce, ya na fama da Talauci ne sosai, domin a da ya na da shanu guda 70 da ya gada a gidansu kuma a ka kwace ma sa su a yankin Taraba, a ka kuma kashe ma sa makiyayin, sannan a ka kashe ma sa babban dansa mai shekaru 12.
Ya kuma ce, a baya ne lokacin da ya je kasuwar Iware a Jihar Taraba yayin dawowar da zai yi sai ya tarar da wannan aika-aikar da a ka yi ma sa ta kisan, a ka kuma kwashe shanun a ka yi gaba da su. Shi ne sanadiyar shigarsa wannan hali na kuncin rayuwa da ta sa shi  fitowa ya furta wannan kalami.
Usman ya ce, saboda bai da aikin komai a can Jihar Taraba, sai ya dawo Gombe ya nemi aikin gadi a unguwar GRA a na biyan sa albashi na Naira 20,000, amma a cewarsa kudin sun yi ma sa kadan, saboda ya na da ‘ya’ya uku da matarsa daya.
Ya ce, shi ne ya sa a ka dauke shi a hoton bidiyon, ya kuma bada izinin a tura a shafin sada zumunta na Facebook, don wadanda ya yi barazar su gani, don su neme shi.
“Ban yi wannan furucin da gaske ba; na yi ne da niyyar gwamnati ta kalle, ni ko zan samu tallafi a rayuwa, saboda yadda na gaya ma ka Ina cikin bakin talauci,” in ji Usman.
Ganin ya aikata wannan laifi da ’yan bijilante su ka kama shi za su mika shi ga hukuma, ya ce, ya na neman a yi ma sa afuwa; ba zai sake ba, domin kuskure ne.
Da ya ke bayyana yadda su ka kama  shi, Kwamandan ’Yan Biilante na Jihar Gombe, Abdullahi Ibrahim Dan Asabe, cewa ya yi, ya na zaune a ka kira shi a ka gaya ma sa cewa, ga wani bidiyo da ka tura a Facebook ya na yawo a na barazar kisa ga Gwamna Inuwa da Shugaban kasa su nemo shi. Shi ne ya baza yaransa cikin farin kaya, ya ba su awa 24 su nemo shi da ikon Allah kuma cikin awa shida su ka samu wanda ya san shi, su ka kama shi a wajen da ya ke aikin gadi.
Abdullahi Dan Asabe ya ce, wannan idan a ka bar shi irinsa ne su ke zama masu garkuwa da mutane, don karbar kudin fansa ko ’yan ta’adda.
Ya ce, a lokacin da su ka kama shi ya musanta cewa, ba shi ba ne ya furta wannan kalaman, amma sanda su ka kunna ma sa waya ya gani, sannan ya yarda ya amsa laifinsa.
Kwamandan ya ce, yanzu za su mika shi ga DPO na kwaryar Gombe, shi kuma DPO zai mika shi zuwa ga Kwamishinan ’Yan Sanda, sannan su kuma su su ka san yadda za su yi da shi.
Ganin aikin bijilante aiki ne na sa-kai da ba a biyan su kuma ga irin kokarin da su ke yi, ya yi kira ga Gwamna Yahaya da ya taimaka ya dinga ba su alawus-alawus da kuma samar mu su da kayan aiki da zai taimaka mu su ya kara mu su kwarin gwiwa su yi aikin sosai, domin yanzu haka ko babur ba su da shin a aiki, balle motar sintiri.
Abdullahi Dan Asabe, ya kuma kara da cewa idan su ka samu kayan aiki za su iya kawo karshen ’yan ta’adda da Yan kalare a jihar Gombe cikin watanni shida da kuma taimakon al’ummar jihar.
Sannan sai ya godewa jama’ar jihar da irin hadin kai da suke basu inda yace idan ba’ayi sauri an shawo kan irin wannan matsalaloin ba ganin kwaya ta yi yawa za ta kai a zama kamar Zamfara ko Katsina wajen ta’addanci.
Daga nan Abdullahi Dan Asabe, ya kara yin roko na musamman ga gwamna Inuwa Yahaya da idan ya taimaka musu da kayan aiki yana mai tabbatarwa da gwamna za su bada gudumawar su yadda ta kamata, ya kuma godewa Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida Dauda Batari, na yadda yake basu kwarin guiwar gudanar da ayyukan su yadda ya dace.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: