Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Kama Wadanda Aka Bankado Su Na Da Rijiyoyin Mai A Gidansu

Published

on

Jami’an binciken bayanan sirri sun kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton a na zargin su da yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Mutane biyun da aka kama, Victoria Ogunsomi, 58, da Shafe Abayomi, an kama su ne a makon da ya gabata a bayan da jami’an binciken sirrin suka bankado wasu rijiyoyin man fetur har guda biyu wadanda su ke shake da man fetur din da ake kyautata zaton suna satarsa ne ta hanyar zuko shi daga bututun kamfanin mai na kasa (NNPC), wanda ya bi ta kusa da gidan na su da ke Surprise Avenue, Ejigbo, Lagos.

An bayar da rahoton cewa an rada wa jami’an binciken sirrin ne a kan miyagun aikin na masu satar man, wadanda su ke durara shi cikin rijiyoyi din da suka haka domin haka, masu zurfin kafa 75 da su ke kusa da bututun man, wanda kuma suka hada shi da wasu motocin tanka da jarkuna domin kaiwa kasuwa.

A gidan Ogunsome, an ce ‘yan sandan sun sami wasu tulunan mai, amma an ce Abayomi ya yi hanzarin kwance su daga bututun da kuma mashin din da ke tunkudo man daga bututun kafin isar jami’an ‘yan sandan gidan na shi.

Majiyoyi sun ce mutanan wajen sukan yi satar man daga bututun man na kamfanin na NNPC wanda ya bi ta cikin unguwar na su.

“Majiyoyi sun shaida mana cewan mutanan unguwar suna da rijiyoyin man ko kuma tankunan karkashin kasa da aka hada su da bututun man na kamfanin na NNPC wanda ake satan man daga gareshi a duk lokacin da kamfanin na NNPC ya ke tunkuda man ta cikinsa zuwa sauran sassan kasar nan, sau tari man na su duk cikin wadannan rijiyoyi da tankunan kasan ne ya ke kwarara, inda su kuma cikin hanzari su ke tura shi zuwa cikin tankokin mai da suka tanada.

“Majiyar ta shaida mana cewa, yawanci da dare ne tankokin man su ke isa wajen domin kwasar man. Da muka bi diddigin rahoton sirrin da muka samu sai muka dirka a gidajen inda kuma muka sami wadannan rijiyoyin man da bututun da su ke janyowa da mashinan tunkuda man a cikinsu zuwa ko’ina.

 
Advertisement

labarai