Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da mallakar harsasai guda 204, mazauna cikin garin Bauchi. jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Mohammed Wakil, ne ya bayyana haka. Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne ranar Lahadi, 14 ga watan Fabarairu, 2021 a Kofar Dumi da ke yankin Bauchi.
Mai magaba da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce, wadanda aka Kaman su ne, Muhammed Sanusi da Abba Sa’idu da Yakubu Ahmed da kuma Sa’idu, dukkaninsu mazauna garin Bauchi.
SP Wakil, ya ci gaba da bayyanawa majiyarmu cewa, babban wanda ake zargin Adamu Suleiman, mai kimanin shekara 50 a wani gida mallakar Hafsat Umaru Tela wanda yake haya a cikinsa.
Haka kuma ya ce, an kama mutum biyu da ake zarginsu das a hannu kan kokarin aikata wannan laifi wato, Muhammed Sanusi da Abba Sa’idu, wadanda kuma su ne suka kawo Adamu Suleiman wannan gida.