An Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Boko Haram Ne A Kasar Sudan

Rundunar sojojin Sudan ta ce ta kama wasu ‘yan kungiyar Boko Haram ‘yan asalin kasar Chadi su shida, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da rundunar ta aike wa AFP ta ce: “Sojojinta masu tattara bayanan sirri sun kama ‘yan kungiyar Boko Haram shida kuma sun mika su ga hukumomin kasar Chadi,” kamar yadda wata yarjejeniya tsakanin kasashen biyu ta tanada.

Kakakin rundunar sojojin Sudan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar (Suna) cewa “rundanar sojojin ta sha alwashin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar kuma za ta ci gaba da gano ‘yan ta’addan da ke kasar”.

Wannan ne karon farko da mahukunta a Sudan suka bayyana kama mayakan Boko Haram a cikin kasarsu.

Kasar Chadi, wadda take da fadin kasa sosai, ta yi iyaka da kasar Sudan daga gabas.

Har ila yau, Chadi tana sahun gaba wajen yaki da kungiyar Boko Haram a yankin sahel.

Kawancen kasashen yankin yammacin Afirka da ke yaki da kungiyar da ya hada da kasashen Burkina Faso da Mali da Mauritania da Chadi da kuma Nijar suna samun goyon bayan dakarun kasar Faransa.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Muammar Gaddafi na Libya ne zaman lafiya ya yi kaura a kasar Libyar take shafar wasu kasashen yankin kamar Nijar da Chadi da kuma Sudan.

Exit mobile version