Connect with us

JAKAR MAGORI

An Kama Wasu ‘Yan Fashi Biyu A Hanyar Ibadan Zuwa Legas

Published

on

Jami’in rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun sun kama wasu‘ yan fashi biyu a daidai gadar Legas-dake kan babbar hanyar Ibadan da Legas, na karamar Hukumar Obafemi-Owode a jihar yayin da suka kwace masu ababen hawa kudade.

Jami’in hulda da jama’a na rudunar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fada ranar Lahadi.

Oyeyemi ya ce, wanda ake zargin Ibrahim Nura, mai shekaru 27, dan asalin Jihar Kebbi, da Isaac Kyegh, daga Jihar Binuwe, an kama su yayin da suke tattare dukiyoyin mutane a kan gadar.

Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun yi wa wadannan mutane fashi ne yayin da suke kokarin gyara motarsu da ta lalace a kan gada.

A cewarsa, ba zato ba tsammani mutanen biyu sun fito daga karkashin gadar inda suka yi barazanar cewa za su sassara su da wukake da adda idan ba su ba su kudadensu da suke jikinsu ba.

Oyeyemi ya ce, “A yayin aiwatar da wannan, tawagar jami’an tsaro ‘yan sintiri daga sashen Warewa, karkashin DPO, SP Folake Afeniforo, wacce ke aikin sintiri ta yau da kullun kan gadar ce ta kama su a cikin lamarin.

“A lokacin da masu laifin suka ga zuwan ‘yan sanda sun kawo simame, sai suka tsallake suka fada kasan gada domin su koma maboyarsu, amma kafin su tsere ‘yan sanda sun cafke su.”

Jami’an hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ya ce an sami adda da wuka daga hannun wadanda ake zargi da aikata fashin.

Ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Kenneth Evrimson, ya ba da umarnin mika wadanda ake zargin nan da nan zuwa ga ofishin jami’ai na musamman wadanda ke yaki da fashi da makami don gudanar da bincike cikin adalci da kuma hukunta su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: